✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har Saudiyya na kai tallar turmi – Sani Mai turmi

Muhammad Sani wani mai sana’ar sassakar turmi ne, ya ce tallar turmi ta biya shi sabanin yadda Bahaushe ke cewa wahala tallar turmi, domin har…

Muhammad Sani wani mai sana’ar sassakar turmi ne, ya ce tallar turmi ta biya shi sabanin yadda Bahaushe ke cewa wahala tallar turmi, domin har kasar Saudiyya ya je tallar turmi kuma ya sayar har ma ya rika sassakarsa a can. Aminiya ta tattauna da dattijon inda ya yi mata bayani kamar haka:

Mene ne sunan malamin?
 Sunana Alhaji Muhammadu Sani Mai turmi kuma ina zauna ne a jikin gidan Radiyon Sarauniya Amina FM da ke Tudun Wada, Zariya, a nan nake gudanar da sassakar turmi ina saidawa, amma asalina mutumin Katsina ne. Kuma wannan sana’a na fara ta ne a gidanmu domin ita na tashi na tarar da iyayena da kakannina suna yi. Tun kafin a yi min kaciya na fara sassakar turmi.
Me da me mutum zai nema kafin ya fara wannan sana’a?
To na farko dai za ka nemi gatari da mahura da gizago da ma’arniya. Gizago shi ne wanda Bahaushe ke ma kirari ‘ba ka da sabo’ mai sassaka tsare hannunka in ka kiya ya ji ma. Ka ji kirarinsa ke nan, sai itace, mu mun fi amfani da madaci da kirya da doka da maje, wani lokaci har da itacen dalbejiya duk muna turame da su domin su suka fi aminci.
Shin nau’in turmi nawa ne?
 Na farko akwai wawu, sai wanda ake ce wa dogon turmi; akwai na dakan sakwara, akwai na sussuka. Dogon turmi da shi ake sakwara da sussuka da kuma aikin tatsar gyada, sai kuma dan karami wanda mata ke dake-dake a cikinsa.
Ina da ina ka kai tallar turmi?
To yaro, na yi yawace-yawace, domin kusan na zagaye kasuwannin Arewacin kasar nan, kuma na shiga kasuwannin kasar Nijar, kamar su Maradi da Tasawa da sauransu. Sannan na je kasar Chadi da Kamaru. Kuma in yi maka ta babban Malam, har kasar Saudiyya na je daga nan na sa turamena a mota guda 53, sai Kano na je aka yi min takarduna da komai na auna kayana a jirgin sama sai Jiddah, muna sauka a Jiddah, to a nan ne fa na sha gwagwarmaya. Sai Balarabe ya daga turmi sama ya sake shi kasa, sun dauka ko kwaya na sa a ciki. Duk suka gama wurgar da turamen nan ko turmi daya bai tsage ba, kuma ba su fashe ba, kuma ba a kama ni da wani kayan laifi ba. To bayan an gama dogon Larabci, sai aka ba ni turamena na sa su a mota sai Baushen Makur.
Ina ne Baushen Makur?
Baushen Makur wani gari ne a Makka (Saudiyya), to nan na kai turamena na baza a kasuwa. Allah Ya taimake ni na sayar kuma na yi aikin Hajjina tsaf, har ma na koma idan an sare itacen dalbejiya, sai in sassaka musu turmi sai da na kwashe wata shida da kwana 14 sannan na dawo Najeriya kuma ba kamo ni aka yi ba, ni na dawo a kashin kaina.
Tun turmi na kamar nawa ka fara saidawa?
Na fara saida turmi tun yana taro, har ya kawo sule, har ya kawo sule da sisi, yanzu zamani ya kawo mu muna saida turmi Naira dubu uku har dubu biyar.
Ko akwai wanda ka koya wa sana’ar?
Na koya wa mutane da dama kuma a yarana da yake maza biyu ne su ma duk sun koya.
Baba wani abin jin dadi ka samu a sana’ar nan?
 Haba yaro, ai ba sa lissafuwa, domin na yi aure, matana uku; yanzu haka yarana bakwai, kuma ina da gida kuma na yi aikin Hajji a ciki, yanzu shekarana kusan 65, don haka ai na karyata maka kalmar nan ta Bahaushe na cewa wahala tallar turmi domin ni dadinta na sha.