✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu a kan batun rufe kan iyakokin kasar nan

Tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta ba da shelar rufe kan iyakokin kasar nan na kan tsandauri a ranar 20 ga Agustan da ya gabata,…

Tun bayan da Gwamnatin Tarayya ta ba da shelar rufe kan iyakokin kasar nan na kan tsandauri a ranar 20 ga Agustan da ya gabata, jama’ar wannan kasa da na makwabtanmu suke ta cece-ku-ce a kan cancanta da rashin cancantar yin haka.

Dalilai biyu gwamnatin ta bayar kan yin hakan, da suka hada da neman kawo karshen sukurkucewar tsaro a kasar nan da aka dade ana ta fama da shi daga irin rikicin tayar da kayar baya irin na kungiyar Boko Haram da na ’yan bindiga zuwa na masu yin garkuwa da mutane don neman kudin fansa da sauran ayyukan ta’addanci da suka game kasa. Sai bazuwar kananan makamai a hannun ’yan kasa da ake zargin ana amfani da su wajen aikata wadancan miyagun ayyukan ta’addanci.

Dalili na biyu shi ne irin yadda ake shigo da kusan komai a kasar nan ta hanyar fasa-kwauri, abin da ke sa kasar asarar biliyoyin Naira da kin biyan kudaden fito yadda ya kamata.

Da farko dai ’yan kasar nan da  makwabtanta sun yi tsammanin rufe kan iyakokin na dan karamin lokaci ne kamar yadda gwamnati ta fada tun farko, amma sannu a hankali sai ga shi tafiya kara gaba-gaba take yi, har ta kai ba wanda zai ce ga ranar da gwamnatin za ta sake bude kan iyakokin.

Kasancewar gwamnatin ta huda ta ga jini, ma’ana kullum mahukunta na ba da lissafin yawan haramtattun kayayyakin da suka kama irin su shinkafa da man girki da fetur da dangoginsa da motoci da makamantansu da kuma karin kudaden shiga, baya ga dimbin bakin haure.

Amma kuma ’yan kasuwar kasashen da ke makwabtaka da mu da namu na cikin gida da suke hada-hadar shigowa ko fitar da kayayyaki ta kan iyakokin kasa sun ci gaba da kokawa kan wannan matakin ba sani-ba-sabo da gwamnati ta dauka, kasancewar gwamnatin ta yi haka ne, ba tare da ta ba wani wa’adi ba, bare a ce sun shirya. Hakan ya sa harkokin kasuwanci, musamman kasuwannin da suke kan iyakokin kasar nan komai ya tsaya cik, ko a ce wasunsu sun daina ci.

Dadin dadawa tunda aka rufe kan iyakokin, motocin dakon kaya na can makare da kayayyakin ’yan kasuwar kowane bangare, suna zaman jiran ranar da gwamnatin za ta dan daga kafa ta bude kan iyakokin, ko da na wucin gadi ne.

Rahotanni sun tabbatar ko yanzu gwamnati ta sassauta matakan nata, to, wasu kayan sun riga sun lalace.

Ba wai ’yan kasuwa da sauran jama’a kadai suke nuna damuwarsu a kan rufe  iyakokin namu ba, har da kasashe irin su Jamhuriyyar Benin da Ghana.

Alal misali a ’yan kwanakin nan, bayan koke-koken Shugaban Kasar Benin, an ji Shugaban Kasar Ghana Mista Nana Addo Dankwa Afuko Addo lokacin da yake karbar ayarin Bankin First Bank da suka kai masa ziyarar ban-girma a kasarsa, karkashin jagorancin Shugaban Hukumar Daraktocin Bankin, Cif Oba Otudeko, yana cewa rufe kan iyakokin kasa da Najeriya ta yi wata babbar koma-baya ce a daidai lokacin da ake fatar kara samun dunkulewa wuri daya a Kungiyar Tattalin Arziki ta Kasashen Afirka ta Yamma (ECOWAS).

Shugaban Ghana, ya nuna takaicinsa cewa a lokacin da Kungiyar ECOWAS, take fuskantar kalubalen yadda za ta bullo da yin amfani da kudin bai-daya a nahiyar, sai kuma ga batun rufe kan iyakokin kasa da makwabtanta da kasar nan ta yi, al’amarin da  ya ce wani babban koma-baya ne ga kasashen ECOWAS din.

A can kasar Ghana, a wani abin da za a kira tamkar ramuwar gayya kan rufe iyakokin da kasar nan ta yi, ’yan kasuwar  Ghana a karkashin kungiyarsu ta GUTA, suna can suna kara rufe kantuna da shagunan ’yan kasuwar kasar nan mazauna kasar Ghana, kamar yadda suka yi ta yi a baya a birnin Accra babban kasar da birnin Kumasi.

Kasuwannin baya-baya da ’yan kasuwar Ghana suka rufe kantunan ’yan Najeriya sun hada da Alabah da Adhye da ta Kejetia da ta Suame Magazine, dukkansu a Lardin Ashanti.

Gwamnatin Tarayya ta bakin Ministan Harkokin Kasashen Waje, Geoffrey Onyeama a ranar 4 ga watan nan a karon farko ta gindaya wasu sharudda da ka’idojin da ta ce sai kasashen da ke makwabta da mu sun cika, kana za ta sake bude kan iyakokinta. Sharudda da ka’idojin, sun hada da dukkan wasu kayayyaki da za a shigo da su kasar nan daga wata kasar Kungiyar ECOWAS, lallai su kasance cikin mazubi ko kwalinsu na ainihi.

Wajibi ne kuma kayayyakin su samu rakiyar jami’an waccan kasa har zuwa kan iyakar kasar nan, kamar yadda suka shigo kasashensu, su kuma damka su ga jami’an  Kwastam na kasar nan. Hakazalika Ministan ya ce lallai kayayyakin da ake yi a kasashen Kungiyar ECOWAS, su kasance ingancinsu ya kai sharuddan da kungiyar ta gindaya.

Wani sharadin da kasar nan ta gindaya kafin a shigo da kayayyakin shi ne muddin kayayyakin a cikin kasashen ECOWAS aka yi su, to su zama suna da inganci, in kuma daga wata uwa duniya ce, to, ingancinsu lallai ya zarta da kashe 50 cikin 100, a kan wadanda ake yi a Afirka ta Yamma. Ma’anar haka inji Ministan bai wuce neman karfafa kasuwanci tsakanin kasashen na ECOWAS ba. Daga karshe Ministan ya ce ya zama wajibi kasashen da ke makwabtaka da mu su rushe dukkan manya da kananan rumbunan ajiyar kayayyaki da suke kan iyakokin wadancan kasashe da kasar nan.

Dukkan wadannan matakai da mahukuntan kasar nan suke dauka yanzu, da ake ganin sun yi matukar tsanani da za su iya kara jefa mutanen kasar nan da na makwabtanta cikin mawuyacin halin da ya fi na yanzu, kowa ya sa ni cewa tuntuni  ya kamata Gwamnatin Tarayya ta dauke su, amma ta yi biris da su. Kazalika sanin kowa ne kasashe irin su China da Birtaniya da Faransa da Japan da Amurka, duk ba su kai fagen shahara da wadatuwar da suke alfahari da ita ta fannin ayyukan gona da kere-kere, da sauran ayyukan ci gaba ba, sai da suka dauki matakai daban-daban, ciki har da rufe iyakokin kasashensu da hana shigo da duk wani abu da suke iya yi.

Bare mu da ba cewa muka yi an rufe kwata-kwata ba. A nan akwai bukatar ’yan Najeriya a kara karatun ta-natsu, mu san ta inda za mu ba gwamnati hadin kan da ya kamata, mu kuma ba ta. Ita kuma gwamnati ta rika yi cikin kamanta gaskiya da adalci, tare da tuntuba da tafiya tare da dukkan masu ruwa-da-tsakin da ya kamata. Ta haka da yardar Allah za mu kai tudun-mun-tsira.