Da Dumi Dumi

Har yanzu ba a gano Magajin Garin Daura da aka sace ba

Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba
Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar Uba

Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ta ce ta samu nasarar kama wadansu da ake zargi da hannu wajen kama Magajin Daura Alhaji Musa Umar Uba inda take ci gaba da gudanar da bincike.

Sai dai Kakakinta SP Gambo Isah bai bayyana sunayen wadanda rundunar ta kama ko abubuwan da ta gano daga wajensu ba.

Ya ce rundunar ba ta ambacin sunayensu ba ne da kuma abin da ta gano a wajensu saboda matsalar tsaro da kuma ci gaba da bincike.

Jaridar Aminiya ta gano yau kimanin kwanaki 45 kenan da aka sace Magajin Dauran da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne amma har yanzu babu labarinsa.

Magajin Garin Daura an sace shi ne a ranar 1 ga watan Mayun wannan shekara a kofar gidansa da ke Layin Daurama a birnin Daura jim kadan bayan an kammala sallar Magriba.

ADVERTISEMENT

Sai dai abin da ke daure wa jama’a da dama kai kamar yadda rundunar ’yan sandan ta nuna shi ne wadanda suka sace shi sun ki tuntubar iyalansa a game da kudin fansa kamar yadda suke yi da zarar sun sace wani ko wasu.  “A gaskiya wannan abin tsoro ne da kuma takaici ganin abin ya dauki tsawon lokaci ba tare da masu garkuwan sun tuntubi iyalansa ko wasu na kusa da shi ba.  Duk da haka rundunar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen zakulo wadanda suka aikata haka sannan za ta yi kokari wajen ceto Magajin Garin ba tare da an samu matsala ba”, inji Kakakin.

Dan Lawan Daura Umar Umar Ata wanda kani ne ga Magajin Daura a zantawarsa da Aminiya ya ce sun shiga mawuyacin halin tun bayan bacewar Magajin Garin.

“Haka muka yi Azumin Ramadan da bikin Sallah cikin kunci, amma dai mun ci gaba yin sadaka da addu’o’i sannan  mun bar wa Allah komai don abin ya fi karfinmu,” inji shi.

Magajin Garin Daura kani ne ga Mai Martaba Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk kuma shi ke auren Hajiya Bilkisu, ’yar uwa ga shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya