Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

…Har yanzu ba mu samu takardar an kai mu kotu ba – Kawuwa Damina

Alhaji Kawuwa Shehu Damina
Alhaji Kawuwa Shehu Damina

Alhaji Kawuwa Shehu Damina mai wakiltar mazabar Darazo, shi ne Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Bauchi a shekara hudu da suka gabata 2015-2019, shi ne kuma wanda ’yan majalisa 18 na Jam’iyyar APC suka zaba.  Ya zanta da manema labarai ta wayar tarho inda ya fayyace matsayinsu kan wannan takaddama na zaben Shugaban Majalisar ga yadda hirar ta kasance.

Ga Alama zaben shugabanbin majalisa ta tara da aka yi a Jihar Bauchi ya bar baya da kura saboda zabar shugabannin majalisa biyu, zuwa yanzu daya bangaren ya ce ya fara tattaunawa da ku don ku  hakura kuzo a tafi tare mece ce gaskiyar wannan lamari?

ADVERTISEMENT

Wannan magana ba gaskiya ba ce kuma gyarar da nake so in yi shi ne mu ne ’yan majalisa guda 31 da Allah Ya sa aka zaba, amma matsalar ita ce magana ce ba ta Kawuwa ba, ba ta ’yan majalisa wadanda suka fito daga APC ba. Magana ce ta uwar jam’iyyarmu ta APC, zama muka yi a matsayinsu na uwa muka yanke hukuncin me ya kamata mu yi? Abu mai sauki ne idan jam’iyyar da ta goya mu muka tsaya takara a karkashinta, jama’armu suka yi mana alfarma suka ba mu kuri’unsu, muka zama abin da muka zama ta kira mu  ta ce kowa ya hakura, to sai a hakura. In kuwa zuwa ta yi ta zo ta ce a yi gyara sai a yi mu kawai biyayya muke yi ba wai ko ’yan majalisa  22 da muka fito daga Jamiyyar APC ba, a’a muna maganar dimokuradiyya ce, yau muna shekara ashirin an sha wahala sosai wajen kafa wannan dimokuradiyyar, al’amura  da yawa suna faruwa ana tunanin yadda za a kara mata inganci bai kamata a same mu wajen ruguzata ba.

Akwai wata takarda da aka samu daga kotu wanda ake sanya ta a kafafen sada zumunta na Intanet cewa kotu ta dakatar da kai da mataimakinka a kan ku bar bayyana kanku cewa ku ne shugabannin majalisar, ko kotu ta ba ku wannan takarda?

ADVERTISEMENT

Gaskiya zuwa yanzu da muke magana da ku ba mu samu ba, ban da a facebook da sauran kafofin sada zumunta na Intanet da wasunmu suka gani. Amma batun gaskiya tsakani da Allah a yadda nake wannan magana ni ko Tukur ko wani daga cikin mambobinmu wallahi ba wanda aka ba wa wannan takarda ta kotu.

A naku bangaren akwai wani mataki ne da kuke ji za ku dauka na zuwa kotu?

Idan kana maganar zuwa kotu ya zama ka yarda da abin da aka yi ke nan. Ka ga wadancan da suka ce sun je kotu sun yarda mu din shugabanni ne. In da ba su yarda ba, ba za su je kotu su kai kara ba, kuma duk da ni ba lauya b ane na ga wata odar tana maganar mako kuma a doka irin ta kasa ba a ba da oda ta kai mako, mu din nan da sauran ’yan  Majalisar Jihar Bauchi a Bauchi muke?  Meya sa aka kai shari’ar Azare?  Gaskiyar magana ba a ba mu takardar kotu ba.