Search
Subscribe
Har yanzu ban kai mahaifina ba a fannin aikin jarida – Hajiya Sadiya Ibrahim Biu

Hajiya Sadiya Ibrahim Biu

Har yanzu ban kai mahaifina ba a fannin aikin jarida – Hajiya Sadiya Ibrahim Biu

Hajiya Sadiya Ibrahim Biu, ’yar jarida ce da ta yi fice a fagen aikin yada labarai. Ta yi aiki da kafafen yada labarai da dama da suka hada da Gidan Radiyon Freedom da ke Kano na wasu shekaru, kafin daga baya ta koma aiki da gidan Radiyon Progress, da ke Gombe, inda a halin yanzu ita ce Janar Manaja na gidan Radiyon da ya shahara a Gombe Progress FM. A zantawar da ta yi da Aminiya, ta bayyana irin kalubale tare da nasarorin da ta samu a rayuwa da ma tasirin da take ganin mata za su yi idan suka shiga aikin na jarida. Ta fara rayuwarta a kasar Amurka, ko da yake ta na aiki a Najeriya amma ba ta fidda ran sake komawa Amurkar da rayuwa ba.

 

Tarihin rayuwata

Sunana Sadiya Ibrahim Biu. An haife ni a garin Biu dake jihar Borno. Ni ce ‘yar fari a gidanmu. Na soma karatun firamare a kasar Amurka, daga bisani na karasa a Legas. Na yi karatun sakandare a FGC Kano, na yi kuma digiri a harshen turancin Ingilishi a Jami’ar Bayero ta Kano.  Ina da aure da yara biyar. Masha Allah.

Sadiya Ibrahim Biu da Iyalanta

Aiki

Na so ma aiki da gidan rediyon Freedom na kano. Yanzu kuma ina Progress rediyo, a matsayin Janar Manaja.

 

Ababuwan da na koya daga iyayena

A gaskiya na koyi ababuwa da dama daga iyayena. Kadan daga cikinsu na koyi hakuri da juriya da jajircewa da sanin ya kamata da sanin zamantakewa da kuma tausayawa na kasa da ni, da dai dai sauransu da dama.

 

Fatana a ina karama

Hmmm, in zama ‘yar jarida kamar mahaifina.

 

Kalubalen da na fuskanta a rayuwa

Gaskiya babban kalubalen da na fuskata shi ne yin karatun digiri na da aure da kuma yara. Ga karatu ga kuma hidimar gida.

 

Nasarorina

Nasarorin rayuwa dai Alhamdulillahi, mun godewa Allah. Kuma na cigaba da samun su. Nasara ta farko shi ne samun Iyaye nagari da suka ba ni tarbiya ta gari dan ganin na zama wani abu a rayuwa. Nasara ta biyu kuma samun miji wanda yake cigaba da bani goyon baya don ganin na cimma burina a rayuwa, sai kuma yara da suke fahimtar yanayin aikina suke kokarin bani hadin kai. Ta fannin aiki ma alhamdulillahi, muna cigaba da jajircewa har yanzu dai ba mu kai inda muke burin kaiwa ba, amma muna ganin sannu a hankali za mu kai ga wurin.

 

Abinda na fi so a tuna da ni

Gaskiya, da hakuri da jama’a da kuma yanayin tausayawa

 

Shawarata ga ’yan uwa mata

Shawarata ga mata ’yan uwana, ba ta wuce mu yi kokari mu ga mun yi karatu, saboda ilmi yana da muhimmanci. Ilmin boko da na addini duk suna da muhimmiaci, don mu Mata mu ne ginshikin rayuwa. An ce idan ka ilmantar da mace daya to kamar ka ilmantar da al’umma. To idan kuwa Mata muka samu wannan ilmi to ina ganin za mu iya sauya alumma gaba daya.

 

Abin da na fi so a rayuwa

To ina son gaskiya, ba na son fuska biyu. Ina jin dadin zama ni kadai wani lokacin in dan yi tunani da nazarina haka.

 

Aikin jarida ga mata

Aikin Jarida ga mata abu ne da yake da kyau, duk da akwai kalubale da matan ke fuskanta a cikin aikin Jaridar. Amma

 

 

shigowarsu aikin yana da muhimmanci, saboda yawan matsalolin da Mata ke fuskanta su ne suke iya shiga su ji ra’ayoyinsu, musamman ma idan aka yi la’akari da matsaloin da ke afkuwa yanzu haka, matsaloli ne  da suka shafar Yara da Mata. To Matan ne za su iya shiga lungu da sako, don su suka san yadda za su yi hira da ’yan uwansu matan dan ganin sun fito da irin wadannan matsalolin a fili. Idan aka duba yawanci mata ne ba su da muryar da za su fito su yi magana. To samun matan a aikin jarida, zai ba su damar su bayyana ra’ayyinsu ga alumma. Sannan kuma za su samu damar gyara matsalolin da suka shafi yara da kuma mata. Idan aka duba ko da matsalolin tashe-tashen hankula da talauci da sauran su, yawanci ya fi shafar Mata da Yara. Saboda haka idan suka shiga aikin Jarida su suka san matsalolinsu kuma su suka san hanyoyin da suke ganin za su taimakawa Mata ’yan uwansu. Saboda haka ina ganin aikin Jarida yana da muhimmanci sosai ga mata. yana da kyau matuka gaya, sa’annan kuma yana taimakawa wajen ganin an samu canji a al’umma sosai.

 

Burina a rayuwa

Burina ina karama har yanzu bai cika ba, da saura gaskiya. Tun ina karama ni ke raka mahaifina lokacin yana aiki a Muryar Amurka, BOA, ni ke raka shi yake labarai. To a wannnan lokacin ni ma na ga cewar ina da burin in girma in ga kaina ina dakin labaran nan. To ina ganin har yandu ina ga da saura, saboda abin da ya yin ya na da girma sosai, don haka har yanzu da saura, muna kai.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin