✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu dai a kan aikin Hajjin bana

Bayan dawowata daga aikin Hajjin bana, na yi wani rubutu game da aikin Hajji a wannan shafi, mai kanun “Aikin Hajji Bana a idanun wanda…

Bayan dawowata daga aikin Hajjin bana, na yi wani rubutu game da aikin Hajji a wannan shafi, mai kanun “Aikin Hajji Bana a idanun wanda ya dade bai yi aikin ba,” inda na kawo bayani a kan yadda na ga kasarSaudiyya bayan na shekara 19 ban je yin aikin Hajji ba. Na kuma kawo bayanai a kan wajabcin aikin Hajjin a kan kowane Musulmi akalla sau daya a rayuwa kamar yadda Musulunci ya shardanta.

Sannan na yi bayanin yadda na ga gyare-gyaren da aka samu a wuraren ibada irin su Mina da wurin jifa da makamantansu, duk dai don samar wa maniyyata sauki wajen sauke farali. Na yi kokarin kawo irin falalar da wanda ya rabauta da yin aikin Hajji ko Umarah kamar yadda Allah Ya yi umarnin a yi, har na kara da cewa alkawari ne Allah (SWT) Ya yi ga bayinSa da suka yi aikin Hajji ko Umarah karbabbe, na yafe musu dukan zunubansu.

Bugu da kari malamai na kara mana da cewar wasu daga cikin alamomin da ke nuna cewa maniyyaci ya dace an karbi Hajjinsa sun hada da mutum ya daina aikata duk wata masha’a da alfasha da aka san yana yi, kafin tafiyarsa aikin Hajjin.

Mai karatu, bayan dawowar tawa na dan yi bincike na kuma ji wasu daga cikin matsalolin da maniyyatanmu suka dade suna fama da su duk da irin yadda mahukuntan kasar Saudiyya suke ta kokarin kawo sauye-sauye don saukaka ayyukan ibadar, amma har yanzu maniyata da suke tafiya ta hannun hukumomin alhazai na jihohi a karkashin kular Hukumar Hajji ta Kasa, har yanzu suna nan maniyyata na fama da su. Abin da ya sa na ce na yi bincike na kuma ji daga wadansu maniyyata, duk da cewa duka-duka kwana 11 na yi a aikin, wanda bai ba ni damar yin cikakkiyar cudanya da maniyyatan kasar nan ba.

Matsalolin da na sani na kuma ji cewa har yanzu Hukumar Hajji ta Kasa da takwarorinta na jihohi ba su iya warware su ba, sun hada da masaukan da jihohi kan kama wa maniyyatansu a birnin Makkah, sabanin na birnin Madinah da Hukumar Hajji ta Kasa ke kamawa a madadin hukumomin jihohi, ta yadda ake zama tare. Har yanzu wadannan masaukai na birnin Makka suna nesa da Harami, sabanin a duk shekarar hukumomin jihohin kan kwadaita wa maniyyatansu cewa, masaukansu na kusa da Harami, amma sai maniyyata sun sauka sai su ga cewa sai sun rika shigo tasi kana za su zo Haramin don yin ibada, ta yadda wadansu ma idan suka zo Haramin da Azahar za ka tarar saboda nisa, sukan zauna har bayan Sallar Isha’i.

Bayan nisa maniyatan sun koka a kan wasu masaukan na Makkah ba su da tsabtar na Madinah ko kusa. Sannan akan samu cinkoson maniyyata ta yadda a wasu dakunan za ka tarar an cunkusa maniyyata 5 zuwa 6, ko 7. Alhali idan aka yi lissafin kudaden da maniyyata kan biya a zaman kudaden masaukai ko kusa bai kamata a yi musu haka ba.

Kodayake maniyyata da dama da na zanta da su sun nuna gamsuwarsu a kan irin abincin da ake ba su sau biyu a rana, na karin kumallo da kuma na dare, abincin da wadansu ke cewa ko a nan kasar ba kowane mai hali yake iya shirya irinsa a kullum ba. Amma kuma wadansu mahajjatan wasu jihohi sun koka a kan karancin abincin bayan kammala Aikin Hajjin, lamarin da suka ce ko a bana an samu haka.

Mai yiwuwa irin wannan karanci abinci, shi ke sa hukumomin alhazai na jihohi in an dawo gida sukan mayar wa maniyyatansu wasu kudade da sukan kira su na wasu ayyukan da ba yi ba. Ko bara Hukumar Alhazai ta Jihar Kano ta mayar wa dukan maniyyatanta fiye da dubu 5, Naira dubu 11 kowannensu. Amma gaskiyar magana ba batun mayar wa maniyyata kudade ne muhimmi gare su ba, babban muhimmin abu shi ne maniyyaci ya samu ingantattun ayyukan da ya biya kudade dominsu a yayin zamansa a Saudiyya.

Yanzu da kudaden guzurin maniyyaci na Dalar Amurka 800, kwatankwacin Riyal din Saudiyya dubu 3, ba su isarsu, kuma a ce bai samu abincin da ya biya tun daga gida ba, ka ga akwai yiwuwar shiga matsala. Wata babbar matsala da maniyyatan kan fuskanta duk shekara, wadda ke neman ta gagari Kundila ita ce ta yawan kwanakin da maniyyatan kasar nan kan kwashe a yayin aikin Hajjin kowace shekara, kwanakin da sukan kama daga akalla 30 zuwa 40 da doriya.

Wannan shafi ya sha kakaci a kan yadda za a gyara wannan matsala, amma ina, don ko a bana ayarin farko na maniyyatan Jihar Kano sai da suka share kwanaki 42. Binciken da na gudanar a kan abin da ke haddasa haka, ya tabbatar mini da cewa tsarin da kasar Saudiyya take amfani da shi na shiga da ficen maniyyatan duniya shi ke haddasa haka. Kasar ta Saudiyya takan sa kasashe su fara shigo da maniyyatansu wata guda kafin ranar fara aikin Hajji, kuma a lokacin shiga kasar akan bari kowa ya sauka ko a filayen jirgin saman Jiddah ko na Madinah, amma a dawowa ta Jiddah kadai kowa zai fitar da maniyyatansa, abin da kan kawo matukar cinkoson sauka da tashi a filin jigin saman na Jiddah.

Ka ga ke nan kamata ya yi kasashen duniya da suke da ruwa-da-tsaki a kan aikin su fara matsa wa Saudiyya lamba wajen ganin ta sassauta wannan tsari, ta yadda za ta rika bude filin jirgin samanta na Madinah kamar yadda aka shiga kasar a fice ta can. Gaskiyar magana ko kadan ba jin dadi ga kowane maniyyaci a ce bayan an yi Arfa an sauko kuma ya yi ta zaman jiran ranar dawowa gida. Wadansu ma ta irin wancan zaman suke bata aikin Hajjinsu Allah Ya sauwake.

Akwai kuma matsaloli irin na sakacin wasu hukumomin alhazai na jihohi da har yanzu duk da irin wannan dogon zaman da maniyyatansu kan yi, amma sai ta kasance ba su samun kwanakin nan bakwai na al’ada da maniyyatan kasar nan suka saba yi a Madinah ba. Wadansu sai ka ji sun samu kwana bakwai, wasu biyar, kai wasu ma kwana biyu aka ce suke samu a zaman na Madinah. Lallai ya kamata hukumomi su kara kulawa da wannan. Abin da ya sanya nake wannan tsokaci bai wuce sanin da na yi na wannan gwamnatin mai son a yi daidai ce a komai ba. Bugu da kari kuma hukumomin alhazai tun daga tarayya har zuwa na jihohi, su sa ni ko ruwa suka ba maniyyaci a lokacin aikin Hajji daga cikin kudaden da ya biya ne, ba alfarma aka yi masa ba. Idan kuma ya yi addu’a a kan an zalunce shi, to fa Allah zai karbi addu’arsa da gaggawa ba tare da wani shamaki ba.