Aminiya

Har yanzu Liberpool na bin Barcelona bashin Naira biliyan 37 a kan Coutinho

Wani rahoto da kulob din FC Barcelona na Spain ya fitar a ranar Lahadin da ta wuce ya nuna har yanzu kulob din Liberpool da ke Ingila yana bin sa bashin Yuro miliyan 94.6 (kimanin Naira biliyan 37 da miliyan 595) game da cinikin dan kwallon Liberpool Philip Coutinho wanda ya canja sheka zuwa kulob din a 2017.

Kulob din ya ce baya ga Liberpool, wasu kungiyoyi da ke bin sa bashi sun hada da Yuro miliyan 30.3 na kulob din Bordeaud na Faransa a kan dan kwallonsu Malcom da Yuro miliyan 10.9 ga kulob din Bayern Munich na Jamus a kan Arturo Bidal da Yuro miliyan 31.4 ga kulob na Balencia na Spain a kan Neto da kuma Yuro miliyan 48.62 ga kulob din Ajad na Holland a kan Frenkie de Jong.

ADVERTISEMENT

Sai dai tuni Barcelona ta tura Coutinho zuwa kulob din Bayern Munich na Jamus a matsayin aro saboda rashin kokari tun bayan da ta saye shi.

ADVERTISEMENT