Search
Subscribe
Har yanzu mata ba su da goyon bayan samun takarar mukaman siyasa – Baheejah

Hajiya Baheejah Mahmood

Har yanzu mata ba su da goyon bayan samun takarar mukaman siyasa – Baheejah

Hajiya Baheejah Mahmood Abdullahi ta tsaya takarar gwamna a zaben da ya gabata. Kasa da mako guda kafin ranar zabe ta janye takararta kuma ita ce  ta kirkiro Hukumar tallafa wa marayu da marasa galihu ta Jihar Bauchi. Cikin wannan zantawa da ta yi da Aminiya a Bauchi, ta yi bayanai kan abubuwan da suka shafi mata a siyasa da kuma fatanta ga gwamnati mai shigowa a Jihar Bauchi:

A baya kin tsaya neman takarar Mukamin Gwamna a Jihar Bauchi, sai gashi kin janye daga karshe ko me ya faru?

Bisa gaskiya lokacin dana tsaya takara bani, nace zan tsaya don kaina ba a a ’yan uwa  mata da maza da matasa ne dama dattawa suka ga cancanta na suka fito cikin kungiyoyinsu da dama suka nemi in tsaya, saboda sun tabatar da cewa ina da kishin Jihar Bauchi, ina da kishin Mata da Matasa da Marsa Galihu musamman bisa la’akari da irin kwazon da na nuna lokacin da na rike da hukumar kulawa da marayu da marasa Galihu ta Jihar Bauchi, Wannan Hukuma ni na kirkiro ta na rubuta duk abinda yakamata ayi mata da goyon bayan gwamnan Bauchi na wancan lokaci, yakuma kai majalisa akayi doka ta zama hukuma, suma marayu da marasa galihu muka nema musu hurumin da za a saurari kukansu a jihar Bauchi.

kungiyoyin da suka zo sun bani hujjoji da dama da suka hada da cewa masu fitowa suyi zabe a Nijeriya mafi yawansu mata ne , kuma tunda nayi rawar gani a baya sun tabbatar dacewa in har na tsaya mata zasu fito kwansu da kwarkwatarsu su goya mini baya, Kuma na amince na shiga takarar ne bisa la’kari da cewa gaskiyane Jihar mu ta Bauchi na cikin wani mawuyacin hali da yake neman Jajirtaccen mutum yazo ya fitar da alummar jihar daga cikin kangin da suka samu kansu a ciki, na talauci da wahala da rashin aikinyi, rashin ayyukan raya kasa, kai ko noma da mafi yawan al’ummarmu suka sa bayi basa iyayi don talauci da rashin kayayyakin noma, ni kaina na amince na fito takarar gwamnane  saboda kishin kasa da kyakykyawar niyya na fito, bayan nayi shawarwari da dukkan wadanda suka kamata , karka mance cikin yan takarar gwamna 31 da suka fito takara a jihar Bauchi ni ce kadai mace. sauran duk 31 dinan mazane da sukayi mini taron dangi ko ince taron jinsi. Kasan yadda Jihar mu ta Bauchi take akwai addini kuma cikin shawarwarin da mukayi har yanzu akwai wadanda ke gani mace bai kamata tayi shugabanci ba , duk da cewa sun yarda tayi kwamishina, tayi minista tayi shugaban maaikata har ma shugabannin kungiyoyi da manyan sakatarorin gwamnati duka mata nayi wannan batun kyamar mace a shugabanci din nan yana daya daga cikin dalilan janyewata bisa taron dangin da maza su kayi mini da yawansu sunyi kokarin mai dani baya kan haka, na biyu siyasa har yanzu ba zai tafi ba a Nijeriya sai an hada da kudi.

Akwai radadi a zuciya da jiki lokacin da dan takara zai janye takararsa zai tuna abubuwa da yawa masoyansa dake goya masa baya,ga kuma uwa uba matsi daga kowani lungu da sako, duk wani wanda kake ganin girmansa ko mutuncinsa za’a bishi don ya saka ka janye,a dakatar da takararka duk ire iren wadannan sune sukasa dole kayi biyayya, Amma a ganina har yanzu ba’a tana darwa mata gurbi a siyasa ba, musamman wajen goya musu baya su tsaya takara  ko da yake a Jihar Kaduna bana Gwamnan JIhar ya dauki mace a matsayin mataimakiyarsa, sai dai zuwa gaba kuma, don haka nayi karatu dabam dabam.

Kamar Yaya ?

Na farko akwai dan takara wanda zai shiga takarar neman mukamin Gwamna tun da farko bada gaske yake yi ba, ya shiga don kawai a kira shi a tattauna da shi a bashi kudi ya janye, akwai kuma dantakara dake da kudin yin takara kuma zai tsaya da gaske, amma alummarsa ba sa sonsa kaga wannan ma rashin hadin kan masu zabe na iya tilasta masa ya janye takararsa. Na uku kuma akwai wanda zai tsaya saboda Allah, saboda kishi, amma kudi ya gaza masa magabata da ‘yan uwa su matsa masa ya janye wa wani dukka wadannan na gansu kuru kuru da idona a siyasar data gabata.

Me zaki ce kan sabuwar gwamnati mai shigowa a Jihar Bauchi?

Alhamdulillahi sabuwar Gwamnati muna yi mata addu’ar alheri muna fata idan zababben gwamna ya kama mulki zai yi namijin kokari ya hada kan alummar Jihar Bauchi, wajen guda ya sanya kwararru a kowace ma’aikata da zasu taimake shi gudanar da mulki a yi Nasara , ya fito da tsare tsare da ayyuka masu yawa da zasu kawo ci gaba a jihar nan, na tabbata mutanen JIhar Bauchi sun zabi mutumin kirki da zai iya yin iyakacin kokarin sa don ciyar da Jihar gaba. Kuma yasa ido ayi gaskiya.

Ko kin gamsu da rawar da mata ke takawa a siyasa ?

Aa kamar yadda na fada a gaskiya har yanzu mata basu sami goyon bayan da ya kamata a basu ba, a fagen yin takara a siyasa ko mukamai da aka ce an ware musu kashi 30 cikin siyasa,ai mukaman da aka tana da musu  baya kaiwa haka don haka da sauran aiki, ga kuma ire iren abubuwan dana fadi a baya yadda ake take su ta amfani da al’ada da addini.

 

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin