✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Har yanzu ‘yan kasuwar waya ta Farm Centre ba su bi doka ba – KAROTA

Bayan wa’adin wata uku da Hukumar Kula da Harkokin Hanya ta Jihar Kano (KAROTA) ta bayar ga ’yan kasuwar wayar hannu ta Farm Centre a…

Bayan wa’adin wata uku da Hukumar Kula da Harkokin Hanya ta Jihar Kano (KAROTA) ta bayar ga ’yan kasuwar wayar hannu ta Farm Centre a kan su bar  kasuwar tare da komawa sabuwar kasuwar da ake ginawa ta Kanawa International Market da ke Dangwaro a kan titin Zariya hukumar ta sanya wa ’yan kasuwar wasu sharudda wadanda ta ce har yanzu akwai sauran rina a kaba.

A lokacin da yake zantawa da Aminiya Shugaban Kasuwar Alhaji Tijjani Musa, ya ce ’yan kasuwar sun yi tarurruka daban-daban da shugabanni a kan batun komawa sabuwar kasuwar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi musu tayi, inda  aka sanya wasu sharudda da ake neman ’yan kasuwar  su cika su.

A cewarsa sharuddan sun hada da bude hanyoyin da ’yan kasuwar suka cunkushe da kuma sauran sharuddan da ’yan kasuwar ke kan cikawa.

“Bayan mun samu takardar izini kan mu tashi daga wannan kasuwa mu koma kasuwar Kanawa, saboda bin doka mun gudanar da tarurruka da dukkan masu ruwa-da-tsaki inda muka cimma yarjejeniyar ta hanyar sanya mana wasu sharudda da muke kokarin ganin mun cika su inda a yanzu muka tashi ’yan kasuwarmu daga kan hanya wadanda a da suka cunkushe kasuwar,” inji shi.

Kakakin Hukumar KAROTA ya ce Gwamnatin Jihar Kano tana kokari wajen ganin dukkan ’yan kasuwa a jihar sun gudanar da kasuwancinsu bisa jin dadi ta hanyar da ta kamata, hakan ya sa ta yi kokarin tsugunar da ’yan kasuwar a sabuwar kasuwar da ke Dangwaro.

A cewarsa duk da cewa an sanya wa ’yan kasuwar sharudda sai dai hukumar ta kula cewa ’yan kasuwar ba su bin sharuddan yadda ya kamata. “Babu shakka mun sanya wa ’yan kasuwar sharudda, duk da cewa ’yan kasuwar sun gyara hanyoyin cikin kasuwar amma sai muka lura cewa an sake ba ’yan kasuwar wasu wurare da ba sa bisa ka’ida. Mun jawo hankalinsu a kan haka muna kuma tsammanin za su bi doka da kuma sharuddan da aka gindaya musu sau da kafa,” inji shi