Search
Subscribe
Harajin Jihar Legas ya fi na jihohi 33

Gwamnan Jihar Legos, Akinwunmi Ambode

Harajin Jihar Legas ya fi na jihohi 33

Kudin haraji da Jihar Legas ke samu ya karu da kimanin Naira biliyan 33 a cikin shekara hudu, lamarin da ya sanya ta doke harajin da jihohin kasar nan 33 suke samu idan aka hade su wuri daya.

Wani bincike da Hukumar Kula da Al’amuran  Kudi da Masana’antu na kasar (NEITI) ta gudanar, ya ce a cikin shekara guda Jihar Legas ta samar da kudin shiga na Naira biliyan 301 da miliyan 190, abin da ya sanya aka samu karuwar kimanin Naira biliyan 33, fiye da jimillar kudin shiga da jihohin kasar nan 33 suka samar na Naira biliyan 299 idan aka cire jihohin Delta da Ogun da Ribas.

Jihar Ogun ta samar da Naira biliyan 56 da miliyan 300 yayin da Delta ta samar da Naira biliyan 44 da miliyan 890. Sai Jihar Ribas da ta samar da Naira biliyan 82 da miliyan 100 na haraji. Idan aka dabe wadannan jihohi 3, sauran jihohin kasar nan 33 sun gaza samar da kudin shiga da Jihar Legas kadai ta samu.

Bayanan Hukumar NEITI sun tabbatar da cewa jihohin kasar nan ba su iya tattaro kudin haraji na a zo a gani, domin Jihar Legas da Ogun ne kadai ke iya samar da kudin haraji da ya zarta kudaden da suke samu daga Asusun Tarayya.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin