Search
Subscribe
Haramcin ba zai sauya komai a gwagwarmayarmu ba – IMN

Wadansu daga cikin ‘ya’yan Kungiyar IMN mabiya Zakzaky, yayin zanga-zanga a Abuja, a makon jiya

Haramcin ba zai sauya komai a gwagwarmayarmu ba – IMN

Kungiyar Harkar Musulunci a Najeriya (IMN) ta ’yan Shi’a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky ta ce haramta kungiyar da Gwamnatin Tarayya ta ayyana a wannan mako ba zai sauya komai ba game da gwagwarmayar da suke yi da gwamnatin.

Jigo a kungiyar kuma Shugaban Gidauniyar Shahidai ta IMN, Malam Abdulhamid Bello ne ya bayyana haka a yayin da yake amsa tambayoyin Aminiya kan dokar da gwamnatin ta sanar, bayan samun hukuncin wata kotu a kai.

Malam Abdulhamid Bello ya ce abubuwan da ’yan kungiyar ke aikatawa harka ce ta akidar addini da suka ginu a kai kuma a cewarsa, duk wani yunkuri na hana su yin sa tamkar gusar da rayuwarsu ce. Ya musanta zargin cewa da dama daga cikin mambobin kungiyar suna tafiyar da al’amuransu gaba-gadi kuma kara-zube, ba tare da sauraron tsawatarwar jagorori a cikinsu ba. Ya bayyana zargin a matsayin sharri da neman bata musu suna.

Ya ce “Ai duk wani bangare da ka gani a cikin wannan tafiyar yana da jagora kuma da a ce haka nan muke tafiya kara-zube ba tare da masu jagorancin tafiyar ba, da gwamnati ba ta sha da dadi ba.”

Haka ya ce a dukkan zanga-zangar da suke gudanarwa akwai wadanda suke kula da sha’anin motoci ta hanyar ba da hannu, inda ya ce masu motoci na gudanar da harkokinsu ba tare da fuskantar wata kuntatawa daga wajensu ba. Saboda haka ya ce ba gaskiya ba ce zargin da ake cewa suna kuntata wa sauran al’umma da ba su ji ba ba su gani ba.

“Idan kuwa suna ganin wannan muzahara da muke yi ta kuntata musu, to sai su yi hakuri kawai su sako mana jagora, idan suna son sararawa ta wannan bangare. Saboda ba yadda za su zalunce mu sannan su yi tsammanin za mu yi shiru,” inji shi.

Game da rahotanni da ke cewa ana gudanar da sulhu a tsakanin gwamnati da kungiyar kuwa, malamin ya ce “Kofarmu a bude take kamar yadda addini ya bukata, a duk lokacin da suka neme mu. Ai dama su ne suke ganin suna da karfi ba su bukatar sulhu kuma koda muke gudanar da wannan muzahara, ai muna kuma tuntubar wadansu manya a gefe guda.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin