✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Haramta wa wasu shiga Amurka: Ana musayar yawu tsakanin Atiku da BMO

Gwamnatin Amurka ta sanar da haramta izinin shiga kasar ga wadansu ’yan Najeriya da ta ce suna da hannu a yi wa dimokuradiyyar kasar nan…

Gwamnatin Amurka ta sanar da haramta izinin shiga kasar ga wadansu ’yan Najeriya da ta ce suna da hannu a yi wa dimokuradiyyar kasar nan zagon kasa a zaben 2019.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce matakin ba zai shafi gwamnatin Najeriya ko daukacin ’yan Najeriya ba; amma zai shafi wadanda suka yi yunkurin bata zaben watan Fabrairu ne kawai.

Da yake mayar da martani kan hanin dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce wannan hani ya tabbatar da ikirarinsa na cewa an tafka magudi a zaben watan Fabrairu.

Ya bayyana haka ne a wata sanarwa da kakakinsa, Paul Ibe ya fitar a shekaranjiya Laraba, inda ya ce, “Duk da irin fashin zabe da rana tsaka da aka tafka, gwamnatin Buhari da ’yan kanzaginta suna ta kokarin musanta abin da yake a zahiri.”

Atiku ya ce ramin karya kurarre ne; kuma wata rana lallai sai gaskiya ta yi halinta.

Sai dai a martanin Kwamitin Labarai na Buhari (BMO) cewa ya yi wannan takunkumin da aka sanya wa wadansu ’yan Najeriya ya nuna karbuwar Shugaba Buhari a kasashen duniya.

A wata takarda da Shugaban BMO, Niyi Akinsiju da Sakatarenta Cassidy Madueke suka sanya wa hannu, ta ce, “Mun samu labarin takunkumin da Amurka ta sanya wa wadansu da ake zargi suna da hannu wajen kawo tsaiko a zaben da ya gabata. Amma Amurka ta yi bayanin cewa ba tana nufin gwamnati ba ce da wannan takunkumin. Hakan ya wanke gwamnatin Shugaba Buhari duk da kokarin da wadansu suka yi na ganin sun bata sunan gwamnatin.”