Da Dumi Dumi

Hari kan matatar man Saudiyya ya haifar da tankiya a Gabas ta Tsakiya

A murka ta fitar da wasu hotunan tauraron dan Adam sa’annan ta bayyana wasu bayanan sirri da suka samu da ke nuna cewar kasar Iran na da hannu wajen kai hari a matatar man fetur na Kamfanin Saudi Aramco na  kasar Saudiyya.

Tuni dai kasar Iran ta musanta zargin hannu a harin da ’yan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan kasar Iran  suka yi ikirarin kaiwa.

To sai dai wadansu jami’an kasar Amurka da ba a fadi sunayensu ba da suka zanta da kafafen watsa labaran Amurka da na duniya, sun ce bisa la’akari da girman harin ya sa su kokwanton ’yan tawayen Houthi ne suka kai shi.

Sakamakon harin dai ya janyo raguwar danyen man fetur a duniya da kashi biyar sa’annan farashin ya yi tashin gwauron zabo.

Me Amurka ke fadi?

ADVERTISEMENT

Sakataren Harkokin Wajen Amurka, Mista Mike Pompeo ya zargi Iran da hannu a harin ba tare da nuna wata kwakkwarar hujja ba, al’amarin da ya tilasta wa Iran bayyana Amurka da mayaudariya.

Da yake bayani a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, Shugaba Donald Trump bai fito karara ya zargi kasar Iran da kai harin ba, amma ya nuna yiwuwar daukar matakin soji a kan duk wanda aka samu da laifin kai wannan hari.

Wadansu jami’an kasar Amurka da ba a bayyana sunayensu ba sun zanta da jaridar New York Times da gidan talabijin na ABC da kuma Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters.

Wani jami’in ya ce Kamfanin Aramco ya samu matsaloli guda 19 sa’annan an kai harin ne daga Yamma maso Arewacin ginin wato ba daga bangaren da ’yan Houthi ke iko da shi ba a Yemen.

Hakan kuwa inji jami’an na nuna yiwuwar kai harin ne daga yankin Tekun Fasha ko kuma daga Iran ko Iraki.

Iraki dai ta musanta kai harin daga yankunanta.

Tuni dai kasar China ta nemi kasashen su mayar da wukakensu kube.

Ita ma Birtaniya ta bakin Sakataren Harkokin Wajenta, Dominic Raab ta ce babu takamaiman wanda za a dora wa alhakin kai wannan hari da ya bayyana da ‘karya dokokin kasa da kasa.’

Martanin  Iran

Har yanzu dai Iran ba ta kai ga mayar da martani ba game da sababbin batutuwan da Amurka ta yi a kan harin

To sai dai Ministan Harkokin Wajen Iran, Jabad Zarif ya wallafa a shafinsa na Twitter inda yake yin shagube ga Mista Mike Pompeo cewa “Sakamakon kasa matsa wa Iran lamba Sakatare Pompeo ya koma amfani da yaudara.”

Jabad Zarif yana nuni ne ga batun da gwamnatin Donald Trump ta yi na amfani da ‘karfi fiye da Kima’ wajen kakaba wa Iran jerin takunkumi tun bayan da Amurka ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Yadda aka kai harin

An dai kai harin ne ranar Asabar kan Abkaik, wurin da shi ne wurin sarrafa danyen mai mafi girma a duniya da kamfanin mai mallakar kasar Saudiyya, Aramco ke kula da shi da kuma rijiyoyin mai da ke Khurais.

Saudiyya ta ce jirage maras matuka ne suka kai harin da misalin karfe 4:00 na dare agogon Saudiyya, inda hayaki ya turnuke.

’Yan tawayen Houthi sun ce dakarunsu ne suka aike da jiragen marasa matuka guda 10 zuwa wuraren kuma tun lokacin sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar karin wasu hare-hare.

Ba a samu rahotannin jikkata ba, to amma har yanzu ba a iya tantance irin barnar da harin ya yi a wuin ba.

Fargabar da ta biyo bayan harin

’Yan tawayen Houthi sun dauki alhakin kai harin; Amurka na zargin Iran da hannu a ciki; Iran ta nesanta kanta daga harin.

Musayar yawun da aka yi ta biyo bayan harin da aka kai wa matatar mai mafi muhimmanci ta kasar Saudiyya

Hare-haren sun nuna irin gagarumin hadarin da ke fuskantar matatun man, masu matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.

Kasar Saudiyya – wacce ke da goyon bayan Amurka, wadda kuma sojojin Yammacin Duniya ke tuka jiragen yakinta – ta dade tana kai hare-haren sama a kan ’yan tawayen Houthi.

Amma yanzu ’yan tawayen sun nuna cewa su ma za su iya mayar da martani da kansu.

Babu shakka hare-haren na ’yan Houthin sun sake dawo da cece-ku-ce game da irin taimako da tallafin fasahar da Iran ke bai wa ’yan tawayen.

Hare-haren sun kuma kara kawo fargaba a yankin Tekun Fasha da ke fama da zaman dar-dar. Sun kuma fito da gazawar gwamnatin Trump na Amurka a fili, wajen aiwatar da tsarin amfani da matsanancin karfi a kan Tehran.

Yayin da ake ci gaba da nuna wa juna yatsa a kan hare-haren, akwai wani abu da babu cikakkiyar masaniya a kai. A baya dai, ’yan tawayen Houthi sun sha amfani da rokoki da jirage marasa matuka wajen kai wa Saudiyya hari.

Kuma a baya hare-haren jirage marasa matuka ba su da wani tasiri. Sai dai kuma dace da nisan zangon hare-haren ’yan tawayen na baya-bayan nan ya sauya tunani kan yadda aka dauki lamarin.

Tambayar ita ce shin da gaske an yi amfani da jirage marasa matuka a harin, ko kuma dai rokoki ne ’yan tawayen suka harba?

Idan har rokoki ’yan tawayen suka harba, to abin tambaya shi ne yaya aka yi shingayen rokoki na Saudiyya ba su yi aikinsu ba?

Shin daga yankunan da ke hannun ’yan Houthin aka harba makaman, ko daga wani wuri?

Shin kungiyoyi da ke mara wa Iran baya a kasar Iraki na da hannu a harin, ko kuma Iran ce da kanta ke da hannu?

Bayan sa’o’i, majiyoyi daga Amurka na cewa an samu wasu hujjoji 17 a kan hare-haren da suke nuna cewa an harba makaman ne daga Arewa ko Arewa-maso Yamma da Saudiyya.

Hakan kuma na nuna cewa daga Iran ko Iraki aka harbo makaman, ba daga Yemen ba wacce ke Kudu da Saudiyya.

Amurka ta kuma yi alkawarin ba da karin haske a kan hare-haren.

Kasar ta kara da cewa tana yin nazari a kan hare-haren wasu rokoki da jirage marasa matuka da suka kasa isa inda aka harba su.

Iran na da kyakkyawar alaka da ’yan Houthi.

Ana kuma kyautata zaton kasar ta taimaka musu wurin mallakar makamai masu cin dogon zango, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka ko rokoki.

A shekarar 2018, rahoton wani kwararre a Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai kamanceceniya sosai tsakanin jirgi marar matuki mai suna Kasef-1 na ’yan Houthi da Ababil-T na kasar Iran.

Binciken ya zargi Iran da karya takunkumin samar da makamai a Yemen, inda ta bai wa ’yan Houthi dabaru da kayan yaki.

A shekarar 2017 ma an gano hakan, bayan nazarin da hukumar da ke bincike kan samar da makamai a rikice-rikice mai zaman kanta ta gudanar, wanda ya mayar da hankali a kan taimakon jirage marasa matuka da Iran ke bayarwa.

Sai dai kuma zangon da Kasef-1/Ababil-T ke ci bai wuce kilomita 100-150 ba.

Amma tazarar da ke tsakanin kan iyakar Yemen da filin hakar mai mafi kusa da ita a Saudiyya kilomita 770 ne.

Saboda haka idan har da jirage marasa matuka aka kai hare-haren, to akwai yiwuwar an sabunta kirarsu, kuma an kara musu nisan zango da nagarta, kamar yadda BBC ya nuna.

 

 

Share