ADVERTISEMENT

Harin bam ya kashe mutum 30 da raunata 42 a Borno- SEMA

Hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Borno SEMA a yau Litinin ta ce a kalla mutum 30 ne suka mutu da raunata wasu mutum 42 bayan da aka kai wasu hare-haren kunar bakin-wake a wani gidan kallon kwallon kafa a talabijin.

An kai harin ne a da daddare ranar Lahadi a Kauyen Mandarari a Karamar hukumar Konduga da ke jihar Borno. Majiyarmu ta samu rahoton kai harin ne da misalin karfe 8:50 na dare ranar Lahadi.

ADVERTISEMENT

Rahoton ya kara da cewa, ‘yan kunar bakin wake su uku ne suka kai harin kunshe da bama-bama, a nan take suka kashe mutum 17 ciki har da jami’in dan sanda.

ADVERTISEMENT