Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Harin bom ya kashe ‘yan gudun hijira 15 a Kamaru

Harin bom ya kashe ‘yan gudun hijira 15 a Kamaru

Mutum 15 sun mutu a wani harin bom da aka kai a a sansanin ‘yan gudun hijira a Jamhuriyar Kamaru da safiyar Lahadi.

Wani jami’an tsaro a yankin ya ce mutum shida sun samu raunuka a harin da ake kyautata zaton kungiyar Boko Haram ce ta kai.

“Maharan sun zo da wata mata da ta shigar da gurnetin cikin sansanin ‘yan gudun hijirar”, inji Magajin Garin yankin Arewa Mai Nisa na kasar Kamaru, Medjeweh Boukar.

Kamfanin dillacin labaru na Reuters ya ambato shi yana cewa harin na kauyen Nguetchewe, mai makwabtaka da Najeriya, ya yi ajalin mata da kananan yara.

Ya ce mazauna yankin sun shaida masa cewa mutum 13 ne suka rasu a sansanin inda mutum 800 ke gudun hijira.

Amma wani jami’in tsaro ya ce karin mutum biyu daga cikin mutum takwas da suka samu rauni sun rasu a asibiti.