✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Iran ya janyo karuwar masu matsalar kwakwalwa a cikin sojin Amurka

Hukumomi a Amurka sun ce adadin sojin kasar da suka samu matsala a kwakwalwarsu bayan harin da Iran ta kai sansanin sojinsu da ke Iraki…

Hukumomi a Amurka sun ce adadin sojin kasar da suka samu matsala a kwakwalwarsu bayan harin da Iran ta kai sansanin sojinsu da ke Iraki a watan Janairu ya kai 109.                     

 

Wadannan alkaluman kari ne mai yawa a kan sojoji 64 da a baya Hukumar Tsaron Amurka ta Pentagon ta ce sun samu rauni sanadiyar harin, kamar yadda BBC ya ruwaito.

Tun farko, Shugaba Donald Trump, ya ce babu wani  dan Amurka da ya ji rauni sakamakon harin.

Harin, wanda aka kai shi ranar 8 ga Janairu, ya faru ne sakamakon rikici da ya barke tsakanin kasashen biyu bayan Amurka ta hallaka Kwamandan Zaratan Sojin Juyin Juya-Hali na Iran, Janar Kassem Soleimani a wani harin sama da sojinta suka kai kan filin jirgin sama na Bagadaza a Iraki.

Kusan kashi 70 na sojojin da suke sansanin lokacin harin sun koma bakin aiki, inji wata sanarwa da Pentagon ta fitar.

Tun farko Mista Trump ya ce ba su ji raunin ba ne a matakinsa na kin mayar da martani ga Iran.

Sai dai a watan da jiy, Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta ce ana samun karuwar masu matsalar kwakwalwa sakamakon raunin da suka ji a lokacin harin, hakan na nufin alamu sun fara bayyana na gagarumar matsala nan gaba.

A ranar Litinin ’yar majalisa a Jam’iyyar Republican, Joni Ernst, ta ce suna bukatar karin bayani kan batun, kamar yadda ta wallafa a shafinta na Twitter.

“Muna da tsarin da muke yi na bai wa sojojin nan kula da yi musu magani kan cututtukan da ke damunsu. Ina kira ga Ma’aikatar Tsaro ta Pentagon ta tabbatar da bai wa sojojinmu da aka kai wasu kasashe kariya da kulawar da ta dace, wadanda suke cikin barazanar samun raunuka sakamakon hare-haren da ake kai musu,” inji ta.

A watan jiya ne Shugaba Trump ya bayyana abin da yake ganin yana samun sojoji idan suka samu kansu cikin dimuwa da kaduwa sakamakon mummunan hari irin wanda Iran ta kai sansanin sojin Amurkar.

“Na ji an ce sukan yi fama da ciwon kai da wasu abubuwa, zan iya cewa ba dai wata matsala ce mai ta da hankali ba,’’ abin da ya fada ke nan lokacin da aka yi masa tambaya kan sojin da lamarin ya rutsa da su.

Da aka kara masa tambaya kan yiwuwar samun tabin hankali, Mista Trump ya ce: “Ba na jin ciwon da suka ji ya yi tsananin da za a alakanta shi da tabin hankali,” inji BBC.