✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harin Nasarawa: Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro kwana 7 a kamo maharan  

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro wa’adin kwana bakwai don kamo ‘yan bindigar da suka kashe mutum 16 a kauyen Numa Kochu…

Gwamnan jihar Nasarawa Umaru Al-Makura ya baiwa jami’an tsaro wa’adin kwana bakwai don kamo ‘yan bindigar da suka kashe mutum 16 a kauyen Numa Kochu da ke karamar hukumar Akwanga.

Gwamnan ya bayar da umarnin yayin ziyarar da ya kaiwa wadanda aka jikkata a babban asibitin Akwanga a jiya Talata.

Gwamna Al-Makura ya kara da cewa, jihar ta kasance cikin zaman lafiya a shekaru uku da suka wuce, don haka gwamnati ba zata lamunci barazanar rashin tsaro a yanzu ba.