✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harkar Tsaro: Yadda ’ya’yan Fulani suka samu kansu cikin harkar fashi (2)

A makon jiya MALAM IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya yi nazari da tsokaci dangane da yadda matasan Fulani suka sauya daga masu tarbiyya da kunya…

A makon jiya MALAM IBRAHIM BABANGIDA SURAJO (08163439197) ya yi nazari da tsokaci dangane da yadda matasan Fulani suka sauya daga masu tarbiyya da kunya zuwa ’yan fashi da makami da sauran laifuffuka, an gabatar da kashi na farko, yau kuma ga karashe:

Abu kamar wasa sarakuna da ardo-ardo suka zama ba su da gashi a idanun wadannaan batagarin matasa. Har ta kai mu yadda ta kai a yau, tare da tallafin barin kan iyakokinmu sakaka. Da kuma yadda aka bar kasuwanni sakaka, ta yadda ta kai a wasu kasuwanni haka za ka ga karar mutane ga kuma ta barayi. Haka dillalai za su je su sayi dabbobin sata a sa a tireloli a yi Kudu da su gaba-gadi.

Bayan sun ida sace dabbobin ’yan uwansu Fulani da suka rage, sai kuma suka waiwayi dabbobin Hausawa makwabtansu na kauyuka da garuruwa, tare da taimakon tsofaffin abokan sharholiyarsu na cikin gari, wadanda ke taimaka musu da bayanan sirri sai su biyo dare su kore dabbobin duk da suke kauye ko gari. Wanda kuma duk ya daga musu yatsa su aika shi barzahu ba tare da bata lokaci ba.

Ta haka ne suke samun kudade su sayi makamai tare da kafa daba a daji wacce suke samar da komai na jin dadi da holewa a ciki. Wannan kuwa ya kunshi mata da kayen shaye-shaye da wutar lantarki, kai har ma da makada da mawaka. A haka sai matasan Fulani suka daina kyamar sata, har ma idan sun ga barawo maimakon su kyamace shi su ce “dun gujjo” kamar a da can baya, yanzu sai dai su yi sha’awarsa su ce “ai ci-ma gaye ne.”

Bayan tsanani ya sanya al’ummomin da wadannan batagari ke damu sun yi kokarin kare kawunansu ta hanyar kafa kungiyoyin banga, wadanda suke fafatawa da maharan. Sai gaba ta yi tsanani aka koma fadan katulan makatulan, ana farautar juna.

Ana cikin haka kuma wane tudu wane gangare sai wadannan batagarin matasa, wadansunsu da suke kai dabbobin sata Kudu don sayarwa suka fara jin labarin wani abu wai shi garkuwa da mutane don neman kudin fansa. Haka suka fara jarrabawa kuma da suka fasa sai suka ga jini. Suka gane ashe ma ga wata hanya mai sauki ta samun kudi cikin ruwan sanyi. Don haka kamar wutar daji sai wannan bakar sana’a ta watsu.

A takaice dai a halin da ake ciki dai ga shi ruwa ya yi tsami. Abin ya gagari kundila, wankin hula ya dauki kwanaki. Ba ga ’yan banga ba, ba ga ’yan sanda ba; har soji zaren na neman bace musu. To amma da yake Hausawa na cewa rashin kira ya sanya karen bebe ya bata, shin ba zai yiwu ba misali Sarkin Musulmi ya tara tun daga kan ardo-ardo da masu unguwa har kan sarakunan wadannan yankuna, su zauna tare su tattauna don gano bakin zaren?

Wato su samo hanyoyin fadakar da al’ummar Fulani da Hausawa irin tsohuwar alaka da ’yan uwantakar da ke a tsakani da kuma muhimmancin da ke tattare da ci gaba da kasancewa ’yan uwan juna.

Ita kuma gwamnati, musamman ta tarayya, shin abin kunya ne a gare ta idan ta fito da wani tsari na musamman kwatankwacin irin wanda Gwamnatin Umaru ’Yar’aduwa ta yi wa tsagerun Neja-Delta na yafiya da ba su damar sake komowa cikin jama’a ta hanyar kulawa da ba da horo na musamman, tare kuma da rika ba su wani dan dauni don samun na kalaci?

Durkusa wa wada ba gajiyawa ba ce, shin kiran wakilan kangararrun Fulanin nan a zauna da su kamar yadda marigayi ’Yar’aduwa ya kira tsagerun Neja-Delta har fadar Shugaban Kasa kasawa ce ga wannan gwamnati?

Na tabbata jama’a da dama za su yarda da ra’ayin da ke cewa babu wanda ake haifa a matsayin mai laifi amma al’umma ce ke cusa masa ra’ayin hakan. Sannan babu wani mutum da yake son a ce shi lalatacce ne tun asali, domin kowa yana da buri da yake son ya cimma a rayuwa. Don haka kangararrun Fulanin nan ma mutane ne kamar kowa, kuma ’ya’ya ne, wadansunsu kuma suna da iyali da ’yan uwa. Ina ganin idan da za a iya zaman sulhu da su, abu ne da ke iya samar da dauwamammen zaman lafiya. Domin idan har zuciyar mutum ta sandare ta kai ga ba ya jin tsoron mutuwa, hanyar kawai da za a zauna lafiya da shi ita ce ta tattaunawa tare da yin sulhu. Domin yanzu kangararrun nan suna ji ne cewa tun daga iyayensu har gwamnati ba mai son su, babu kuma mai kaunarsu. Don haka su ma sammakal. Ya kamata gwamnati tun daga ta karamar hukuma  zuwa ta jiha da ta tarayya, su himmatu wajen sake farfado da madatsun ruwa da shata burtaloli da bullo da wani tsari na bai wa Fulani, musamman wadannan tsagerun kiwon shanu, wadanda za a iya tsarawa duk lokacin da suka yi haihuwar farko ’ya’yan na makiyayin ne, in sun yi ta biyu na gwamnati ta uku na makiyayi.

Sannan uwa uba ya kamata mahukunta su sake duba tsarin karatun nan na makarantun ’ya’yan Fulani da idon basira, domin barin wata al’umma kacokan cikin jahilci babbar barazana ce ga tsaron kasa.