✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Harkoki na daidaita bayan sassauta dokar kulle a Filato

Al’amura sun fara daidaita a Jihar Filato bayan sassauta dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa ta tsawon sa’a 24 sakamakon rikicin da ya…

Al’amura sun fara daidaita a Jihar Filato bayan sassauta dokar hana fita da gwamnatin jihar ta kafa ta tsawon sa’a 24 sakamakon rikicin da ya barke a zanga-zangar #EndSARS.

Rikicin dai ya yi sanadiyyar asarar rayuka da dukiyoyi a ranar Talatar da ta gabata.

Yanzu dokar hana fitar za ta fara aiki ne daga karfe 6 na safe zuwa 8 na dare daga ranar Juma’ar nan.

Mutane na hada-hada a kasuwanni a Jos

Wakilinmu ya gudanar a garin Jos babban birnin jihar Filato ya ga jama’a sun ci gaba da gudanar da harkokinsu na yau da kullum.

Mutane na hada-hada a kasuwanni a Jos

A lokacin da ya isa titin Ahmadu Bello da babbar kasuwar Taminus da hanyar Bauchi da kasuwanni da tashoshin mota da ke garin, ya gane wa idonsa yadda jama’a suka sake bude harkokinsu.

Wasu ‘yan kasuwa da Aminiya ta zanta da su a babbar kasuwar Taminus sun bayyana farin cikinsu, kan yadda gwamnatin jihar ta dauki matakin kafa dokar da sassauta ta ganin kwanciyar hankalin da aka samu.