Search
Subscribe
Hassada ga mai rabo taki ce (5)

Hassada ga mai rabo taki ce (5)

Manyan Gobe da fatan kuna biye da ni a wannan labari. Yau ma ga ci gaban labarin.  Fatarmu za ku yi amfani da darasin da ke cikin labarin.

Nan da nan suka zube  a kasa  suna rokonsa za su zauna  a gidan kuma sun yarda ko wanke-wanke za su rika yi wa Mairo amma atafau maigidan ya ki amincewa, daga bisani ma da ya ga ba za su tafi ba sai da ya yi musu korar kare.

Iyayensu da ’yan uwansu ba karamin bakin ciki suka yi da faruwar wannan lamari ba ganin cewa suna cikin daula amma sun janyo aurensu ya mutu tare da barin daular arzikin da suke ciki,  musamman idan suka tuna  Mairo tana can ita kadai a gidan tana sharvar dadi.

Tun daga wannan lokaci Mairo ta zauna da maigidanta da kuma akunsu cikin koshin lafiya da kwanciyar hankali suna cin duniyarsu da tsinke.

 

Darasin labarin:

Wannan labara yana koya mana kada mu yi wa mutum hassada domin ita hassada ga mai rabo taki ce.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin