Search
Subscribe
Hassada ga mai rabo taki ne (2)

Hassada ga mai rabo taki ne (2)

Manyan Gobe, ga ci gaban labarin da muka faro a makon jiya na hassada ga mai rabo taki ne.

 

Ana nan wata rana  maigidan ya tashi yin tafiya don haka ya yi sallama da matansa da kuma tambayarsu abin da zai sayo musu idan zai dawo kamar yadda ya saba. Kowacce a cikin matan ta gaya masa abin da zai sayo mata amma ban da Mairo.

Jim kadan da tafiyarsa sai ciwon ciki ya murde Mairo ta nemi matan gidan su taimaka mata da magani . Jin haka sai murna ta kama su  ganin cewa ga dama ta samu yadda za su ga bayan Mairo cikin sauki. Maimakon su ba ta magani sai suka dauko  tafarnuwa suka ba ta.

Zafin ciwo ya sa Mairo ba ta gane tafarnuwa suka ba ta ba, nan da nan ta sha ai kuwa sai ciwon ciki ya karu kafin ka ce kwabo sai ta fita daga cikin hayyacinta. Nan da nan suka kwashe ta suka kai ta ban-daki da ma sun haka rami suka binne gawarta a  ban-dakin gidan.

Ashe duk abin da suke yi a kan idon wani akun maigidan suke yi, sai dai bai ce uffan ba . Zuwa can suka tuna da surutun aku sun kuma tabbatar idan har ya gan su to sai ya gaya wa maigidan don haka suka dauki akun suka yi masa dukan tsiya tare da raunata shi daga karshe suka jefa shi cikin wani dakin ajiya da ke gidan.

Ba a jima ba sai maigidan ya dawo inda ya gaya musu cewa har sun yi nisa sai wata matsala ta taso don haka shi da abokan tafiyarsa suka yanke shawarar sai gobe za su yi tafiyar.

Mu kwana nan

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin