Search
Subscribe
Hassada ga mai rabo taki ne (4)

Hassada ga mai rabo taki ne (4)

Manyan Gobe da fatan kuna biye da ni a wannan labari. Yau ma ga ci gaban labarin.  Fatarmu za ku yi amfani da darasin da ke cikin labarin.

Nan dai aku ya kwashe dukkan abin da ya faru ya sanar da mai gidansa. Hakan ya sa mai gidan bai bata lokaci ba ya shiga ban-daki ya ga ramin ya tone sai ga Mairo a ciki tana numfashi sama-sama. Bayan ya fito da ita ya ba ta ruwa ta sha ya kwantar da ita don ta huta.

To duk abin da ake yi matan gidan ba su san abin da ke faruwa ba a tsammaninsu aku ya mutu don haka suka yi banza da mai gidan da nufin idan ya gaji da neman Mairo ya hakura.

Sai maigidan ya kira dukkan matan nasa uku ya tambaye su  me ake yi da makiyi? Gaba dayansu suka hada baki suka ce kisa!

Sai ya sanar da su abin da suka yi wa Mairo tare da sanar da su halin da ake ciki. Ya ce to ni ba zan kashe ku ba amma dukkanku na sake ku kowace ta fita ta bar mini gida.

Mu kwana nan

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin