✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin jirgin kasa ya hallaka shanun N10m

Akalla shanu na Naira miliyan 10 ne suka mutu sakamakon wani hatsarin jirgin kasa a ranar Laraba. Tarago biyu ne suka tsinke a lokacin da…

Akalla shanu na Naira miliyan 10 ne suka mutu sakamakon wani hatsarin jirgin kasa a ranar Laraba.

Tarago biyu ne suka tsinke a lokacin da jirgin kasan ke tsaka da tafiya ya kashe shanu 37 a layin Power Line da ke garin Osogbo, Jihar Osun.

Jirgin na kan hanyarsa ta zuwa Jihar Kwara daga Osun ne taragon suka tsinke suka rika tafiya da baya-baya har suka kade shanun.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Osun, Yemisi Opalola ta ce shanu 41 ne aka kade, 37 sun mutu, hudu kuma sun samu rauni.

Daya daga cikin masu shanun, Ismail Rabiu ya ce asarar da hatsarin jirgin ya ja musu ta kai akalla Naira miliyan 19.