✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hatsarin mota ya ci rayukan mutum 21 a Enugu

Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRCS) ta tabbatar da rasuwar mutum 21 cikinsu har da dalibai, a wani  hatsarin mota da ya auku a yankin…

Hukumar Kiyaye Hadura ta kasa (FRCS) ta tabbatar da rasuwar mutum 21 cikinsu har da dalibai, a wani  hatsarin mota da ya auku a yankin Mgbowo da ke Karamar Hukumar Awgu ta jihar Enugu.

Kwamandan FRSC na jihar, Ogbonna Kalu, ya shaidawa jaridar Punch ta wayar tarho, cewar lamarin ya faru ne a ranar Laraba.

“An rasa rayuka 21 ciki har da wasu dalibai da motar makaranta ke dauke da fiye da dalibai 50.

“Amma daga cikin wanda suka mutu, akwai masu tafiya a gefen hanya”, cewar Kalu.

Ya bayyana cewa bayan bincike sun gano cewar tukin ganganci ne ya haifar da hatsarin inda wata tirela a kan babban titin Awgu ta kwace kuma murkushe motar makarantar da ke dauke da dalibai sama da 50 a cikinta.

Bayan tabbatar da rasuwar mutane 21 an samu wanda suka ji rauni da dama.

Wani ganau ya ce direban motar ya tsere cikin daji ganin irin ta’asar da ya tafka.