✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hattara jiga-jigan Jam’iyyar PDP ’yan kasa na kallonku

Tun bayan zaben shugabannin kungiyar Gwamnoni ta kasa, inda gwamnoni 19, daga cikin 35 da suka yi zaben, suka sake zabar Gwamnan Jihar Ribas, Mista…

Tun bayan zaben shugabannin kungiyar Gwamnoni ta kasa, inda gwamnoni 19, daga cikin 35 da suka yi zaben, suka sake zabar Gwamnan Jihar Ribas, Mista Rotimi Ameachi karo na biyu a matsayin shugaban kungiyar, wasu kuma 16, suka zabi Gwamna  Dabid Jonah Jang na Jihar Filato, a matsayin nasu shugaban, rikici ya kara kazancewa a cikin jam`iyyar ta PDP, har da dakatar da wasu gwamnoni biyu.
Tun kafin aje zaben dama ake ta zargin cewa Shugban kasa Dokta Goodluck Jonathan, ya zuba idanu, kuma ya baza komarsa da taimakon wasu daga cikin gwamnonin da suke goyon bayan takararsa a zaben shekarar 2015, akan lallai-ilallah su tabbatar da cewa Gwamna Ameacni bai sake komawa kan wannan kujera ba, a gefe daya su kuma gwamnoni da suke adawa da yin takarar Shugaba  Jonathan din, suka ja baya suka ce ba za ta sabu ba, wai bindiga a ruwa.
 Wannan ne ya kawo mu a cikin rikicin da gwamnoni da shugaban kasa da shi kansa shugabancin  jam`iyyar suke ciki a yau, al`amarin da ya kai ga yana zubar da mutunci da kimar dukkan mukarraban jam`iyyar ta PDP, musamman masu cikakken iko, duk da sunan sai an mallaki Talakawan kasar nan ta kowane hali.  A takaice dai ana kokarin a koma zamanin mulkin tsohon shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ta “Ko a mutu ko a yi rai.” siyasar da ake ganin lokacinta ya kamata ya wuce.
Alal missali, don bangaren Gwamna Jang su nuna wa duniya da gaske suke akan suke da shugabancin kungiyar gwamnonin, tuni suka bar al`adar da gwamnonin suka kai, ta yin tarurrukansu a masaukin kowane gwamna da ke shugabancin kungiyar na Abuja, suka je suka kama hayar sabon ofis da sunan bangarensu suka bude, ya yin da bangaren Ameachi suka ci gaba da yin taronsu a masaukin Gwamnan Jihar Ribas din. Ga kuma yawan cece-kuce da ake ta samu tsakanin bangarorin biyu, da aniyar kowane bangare ya ce shine halastacce.
 Alal misali dauki abubuwan da suka faru tsakanin shugabannin bangarorin biyu a cikin makon da ya gabata a fadar shugaban kasa. Na farko a ranar Larabar makon jiyan lokacin da shugaban kasa ya gayyaci dukkan gwamnonin jihohi liyafar cin abincin dare a zaman rabin wa`adin mulkinsa, abokan aikinmu manema labarai da ke fadar shugaban kasar sun ruwaito Gwamna Ameachi yana cewa Gwaman Jang da gwamnonin da ba su amince da zabensa ba, ba ma`abota dimokuradiyya ba ne.
Shi kuwa Gwamna Jang da yake mayar da martini ya fadawa manrma labaran fadar shugaban kasar cewa “Don me zan yi rigima da wanda yake tsaran dan da na haifa? dana ne. Na kai shekarun da zan iya kasacewa babbansa: Na kusa cika shekaru 70, don me zan yi rigma da  Ameachi? ” in ji gwamnan na Filato    
Na biyu, a taron Majalisar tattalin arzikin kasa, da akai kashegarin waccan cacar baki, Majalisar da dukkan gwamnonin jihohi suke mambobi. A wajen taron da Mataimakin shugaban kasa Alhaji Namadi Sambo kan shugabanta, an hada gwamna Ameachi da gwamna Jang zama kusa da juna, a karon farko ci. Gwamna Ameachi da ya fara shigowa, ya kuma ga irin yadda aka shirya wurin zaman nasu sai  ya kada baki yace “Yau za a zauna tare, halastaccen shugaba da jabun shugaba.” Can kuma sai ga gwamna Jang, shi ma da ya ga yadda tsarin zaman yake, kafin ya zauna ya budi fuskar gwamna Ameachi, ya yi murmushi, sannan suka gaisa, har suka yi barkwanci.
 `Yan adawa da kasashen duniya duk sun ci gaba da ganin wallen jam`iyyar PDP da Madugunta shugaba da gwamnonita {saboda yawansu} akan irin yadda suka kekasa kasa suka ki karbar sakamakon nasarar da Gwamna  Ameachi ya samu, suna bayyana cewa, to, a zaben mutane 35, ke nan ana neman sai sama da kasa su hade, to, ina ga zaben shekarar 2015, da zai shafi miliyoyin `yan kasar nan.
 Ofishin Jakadancin kasar Nezaland da ke kasar nan shi ya yi suka ta baya-bayan na da ya yi suka akan wannan danbarwa, inda a makon jiya a wajen wani taron yini daya mai taken “Hanyar tabbatar da ingantaccen zabe a kasar nan.” A wajen wancan taro an ji Sakatariya ta daya a ofis din, Mis Akinue Classen, tana tambaya. Idan har wasu gungun mutane 35, ba su iya amincewa kuma su girmama sakamakon zaben da suka yi a cikin dimokuradiyya ba, me zai zama makomar zaben da zai kunshi miliyoyin al`umma?
Shi kansa tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar kuma daya daga cikin wadanda suka kafa jam`iyyar PDP, a wata hira da ya yi da sashen Hausa na gidan Radiyon BBC, a karshen makon jiya,  ya nuna matukar damuwarsa akan irin wannan danbarwar da jam`iyyar tasu ta shiga. Yana mai cewa su  da suka kafa jam`iyyar ba a komai da su, shugaban kasa da gwamnoni su kadai suke abin da suke so cikin tafiyar da jam`iyyar, al`amarin da ya ce ko kadan ba zai Haifa mata da mai ido ba.
Dukkan wannan danbarwa da jam`iyyar ta PDP take ciki, wasu magoya bayanta na cewa ai dama haka ake fuskanta a cikin jam`iyyar da ta cika ta tumbatsa, wai dukkan irin halin da jam`iyyar tasu take ciki za a shawo kansu. Amma Ni a ra`ayina, masu irin wannan ra`ayi ba su ma ganin irin abin kunya da zubar da mutuncin da kama karya da jiga-jigan jam`iyyar PDP suke yi a ciki da wajen kasar nan. Ai kasan wasa ya yi kasa ka ji gwamnoni a jam`iyya daya, kuma mai mulkin gwamnatin tsakiya suna mayarwa da juna martani, har ana batun iyaye, wato dai batu ya kai ga zagi. Don haka nike cewa hattara dai jiga-jigan jam`iyyar PDP, `yan kasa fa suna kallonku.