✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa (13)

Ko kafin nan bincike ya nuna cewa gicciyen da mutanen Agades ke amfani da shi a wajen bauta iri daya ne da na Kibdawan Masar…

Ko kafin nan bincike ya nuna cewa gicciyen da mutanen Agades ke amfani da shi a wajen bauta iri daya ne da na Kibdawan Masar na dauri. Ke nan al’ummar wannan yanki na Guber, ko Gobir ko Gobirawa, Kibdawa ne, Kiristoci kafin su amshi Musulunci. Sun amshi Musuluncin ne kila saboda haduwa da Babas, da suke  makwabtaka da da kuma auratayya da ta hada. Yawancin wannan al’umma da ke zaune a wannan yanki sun auri matan Babas, wadanda yawancinsu Musulmi ne, ta haka wasu suka shiga Musulunci, wasu kuma ta huldar kasuwanci da Larabawa da malamai da suka shigo yankin don watsa addinin Musulunci.
Wane harshe ke nan ake amfani da shi a yankin Guber (Gobir) a daidai wannnan lokaci da muke magana? Masana da dama sun yi ittafaki da cewa harshen daular Guber (Gobir) da ya hada da Kano da Katsina (ko Pauwa ko Wangara) da Zegzeg (Zaria), shi ne harshen Guber ko Gobiranci ko kuma Kibdanci ko kuma gaurayensu.
Wani karin haske kamar yadda masana suka yi nuni shi ne a karni na 16 a cikin harshen daular Songhai,  ana kiran wannan yanki na Guber ko Gobir da Ausa. Tana yiwuwa ke nan daga nan aka sami tushen kalmar Hausa, daga Ausa (Ausawa) kasar Ausa. Sai dai a lura da wani abu a nan, kamar yadda masana suka nuna, shi wannan harshe na Guber ko Gobir ba wai yankin kasar Gobir (ta yau) ake magana kai ba, ana maganar yawancin kasashen Hausa ne kaf dinsu, wato kamar wata daula ce mai dauke da sassa da take mulka.
Wasu masanan kuma sun yi nuni da cewa ba sunan wannan kasa ta Hausa Gobir ba, daga baya ne kila ya koma Gobir din. Irin wadannan masana na kiran yankin da Gungu, wadda ita ma daula ce dadaddiya. Sun yi wannan hasashe ne bisa nuni da irin dangantakar wannan yanki da ciniki na karafa masu daraja irin su Copper. Wanda kuma aka nuna cewa arna ne mazauna wurin kafin su shiga addinin Kirista da Musulunci. Su wadannan al’umma ana kallonsu a matsayin arna ne saboda ba a da wata hujja da ta nuna cewa sun taba saduwa da wani addini na Allah ba ko an taba sada su da wani sako daga Allah. Daga cikin irin wadannan al’umma akwai Maguzawa, da ake nuni da cewa sun sami wannan suna daga Larabawan da suka tako wannan yanki suka same su cikin duhun jahilci da bautar gumaka, haka kuma wasu masana na nuni da cewa cikinsu akwai Dakarkari, domin ita kalmar dakakir na nufin gumaka tun asali.
Idan kuma muka dubi yadda ake rufe gawarwakin shugabanni a yankin da ake wa lakabi da na kasar Hausa ya yi kama da yadda arnan da ke zaune a wasu sassa na wannan yanki ke yi, an ga haka a yankin Gobir da Katsina da kuma Zamfara.
Daga nazarin da masana suka yi wani suna kuma da aka ba wannan yanki na kasar Hausa a cikin littattafan Larabawa da suka ziyarci wannan yanki shi ne Habasha. Sai dai nan ma ya dace a yi bayani mai dan zurfi. Habasha tun asali shi ne sunan da aka bai wa mutanen Abisiniya ko Ethiopia, wato sunan kasa ce mai dauke da daula, kamar Gobir da muka gani a baya. Amma a cikin wasu rubuce-rubucen Larabawa game da yankin Habasha, an nuna cewa al’ummar da ke zaune kudu da Fezzan ko kuma mazauna Yammacin Afirka da ya kunshi daulolin Mali da Songhai da Gobir da zagayensu, su ne Habashawa. Wadannan al’umma ne kuma ake wa lakabi a wasu rubuce-rubucen Larabawa da Sudaniyawa ko bakaken fata.
Bari mu fito da bayanin sarari sosai. Idan har mutanen yankin da ake ce da shi Yammacin Afirka shi ne yankin Habasha da al’ummar Habashawa ke zaune ciki, ke nan akwai dangantaka tsakanin sunan kasar da al’ummar da ke zaune a wurin. Kamar yadda masana suka yi nuni, Habasha shi ne harshen wannan yanki, mutanen kuwa Habashawa. Idan aka yi amfani da kimiyyar harshe za a ga cewa kalmar na iya komawa kamar haka; Bahabashe-Bahabshe-Bahaushe ko kuma Habashawa-Habshawa-Haushawa-Hausawa, kamar yadda yake a cikin karin Katsinanci na dauri. Ba wannan kadai ba hatta dangantakar da ke tsakanin Gobirawa da mutanen Absen ko Abisiniya ko Habasha tun can da kamar yadda wasu masana ke nuni, ya kara tabbatar da wannan matsayi. Wato iyakar kasar Hausa ta dangana da Asben ko Abisiniya, duk alamun gaskiyar batun ne mai nuni da cewa Hausawa Habashawa ne.
A nan ya dace mu yi wa wannan batun namu linzami kamar yadda yawancin masana suka yi a fagen irin wannan bincike. Ba inda muke so mu nuna cewa Hausawa al’umma ce guda, sai dai mun tabbatar al’umma ce da ta wanzu daga tarin al’ummomi masu yawan gaske, wato dai Hausawa gamade ne na al’umomi mabambanta dangane da yankin da suke zaune. Za mu iya cewa Hausawa sun samo asali daga al’ummomi daba-daban, ko kuma mu ce tun can azal, Hausawa Kabbawa ne; Hausawa Kibdawa ne; Hausawa Ausawa ne, Hausawa Gobirawa ne, Hausawa Gungawa ne, Hausawa Habashawa ne. Haka kuma Hausawa Arna ne, Hausawa Kiristoci ne;  Hausawa Musulmi ne, Hausawa Maguzawa ne da makamantan haka.
Abin da za mu yi kila a nan domin daidaita tunani shi ne mu kawo abubuwan da za su iya zama hujja game da ire-iren wadannan hasashe-hasashe da muka yi game da Hausa da Hausawa a doron kasa. Hanyoyin da kuma za su tabbatar da kafuwar wadannan hasashe-hasashe su ne na bin diddigin kalmomin da ke da dangantaka da na wasu harsunan da ke makwabtaka da Hausa da Hausawa ta fuskar al’adu da addini da adabi da sauran sassan zamantakewar yau da kullum.
Za mu ci gaba