✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (12)

Duk wannan bincike me yake son ya nuna mana? Ba wata tantama wannan tsari na sarauta da bauta a Daura haka ya wakana can da,…

Duk wannan bincike me yake son ya nuna mana? Ba wata tantama wannan tsari na sarauta da bauta a Daura haka ya wakana can da, ba wai kawai a kasar Daura kurum ba, har da sauran kasashen Hausa Bakwai, domin alamu sun nuna cewa sarakunan kasar Hausa Bakwai sukan kai ziyara kasar Daura, musamman domin gaishe da Magajiya da bautar al’ada. Ana iya hasashen yadda sarakunan Hausa Bakwai ke ziyartar Magajiyar saboda dangantakar da suke da ita ne ta asali da sarauta, alhali su kuwa sarakunan Banza Bakwai ba sa yin wannan al’ada, amma a can da tana yiwuwa suna zuwa bikin shekara-shekarar, amma ba su gaishe da Magajiya sai dai su leka Iya/Inna a matsayin ’yan uwan Kuyangar.
Baya ga wannan dangantaka da muka gani a tsakanin jiya da yau, akwai karin dangantakar da za a iya gani wadda ta kara nuna irin yadda jiyan kan iya haifar yau din. Mu koma ga Zauren Gani da ake biki a cikinsa a yau, kamar yadda masana suka nuna tun can asali ba bikin gani ake yi a cikinsa ba, nan ne Sarakunan Hausa Bakwai ke taruwa suna tattauna matsalolin kasashen nasu, an nuna cewa akwai matattakala a bayan zauren da kuma babbar taga da Magajiya Daurama ke jan ragamar tattaunawar, akwai kuma wani bango da ke bayan fadar Daura yanzu, nan ne aka ce an kashe macijiyar da ake magana. Idan kuma aka koma ga buga tamburan dajinjin da ake yi duk ranar Juma’a, kamar yadda binciken masana ya nuna, shi ma ya samo asali ne daga yadda Magajiya Daurama da mutanenta ke fita zuwa debo ruwa a rijiyar Kusugu a wancan lokaci. Ke nan idan muka koma cikin tarihi, za mu iya cewa tun can farkon samuwar kasar Daura akwai bangare na Musulmi da Arna, suna kuma rayuwa tare da zamantakewa irin ta zumunci da so da kauna. Duk da wannan dangantaka, ba su zama al’umma daya ba, saboda bambancin tsarin sarauta da kuma mulki. Shi ma wannan tsari kamar yadda bincike ya nuna ya samo asali ne daga abin da al’ummarsu ta gado daga kaka da kakanninsu na can da, musamman daga yankin Gabas ta Tsakiya. Abin da kurum wadannan baki suka yi shi ne ci gaba da yayata abin da suka shigo da shi daga can har ya saje da wanda suka iske, ya zama jiki a tsakaninsu. Saboda haka ko da tarihihin Bayajidda ya kasance tatsuniya ko tarihin kunne ya girmi kaka ko kuma labarai da aka surka karya da gaskiya, abin da masana suka amince shi ne, ko cikin karya ana samun gaskiya, ko cikin labaran kunne ya girmi kaka, ana samun abin da kunnen ya ji, ya karas koda kakannin sun manta da yadda abin ya faru. Ba wani abu ya jawo dakushewa da daukar sakainar kashin da ake wa wannan tarihihi ko labari ba, sai ganin cewa tsawon lokaci ne ya jawo warwarewar da aka yi wa batun da kila gaskiya ne, ko ya taba faruwa, amma rashin ma’adana ta kwarai ya sa ya canja fuska da kamanni a tsawon zamani, kamar yadda masana suka nuna.
Domin karkare wannan tattaunawa da kuma shara fagen bincike, ya dace mu sake waiwaye game da manya-manyan matsaloli da shingayen da ke gaban wannan bincike da kuma samuwar tarihin gaskiya na kasashen Hausa Bakwai da Banza Bakwai.
•    Tun da farko mun aminta cewa Hausawa dai a ko’ina suke, ’ya’ya da jikokin Annabi Adamu da Hawwa’u ne. Jinin kowane mutum a duniya yana dauke da jinin wadannan mutane tun farkon halitta.
•    kwayar halittar dan Adam a yanzu, ita ce a jikin kwayar halittar mahaifansa na farko, ke nan baki da farin fatar mutane na yau, duk daga Annabi Adamu da Hauwa’u suka tusgo. Har zuwa yau wannan kwayar halitta na tattare da mu a duk fadin duniya, ciki har da Hausawa.
•    Annoba da cututtuka a cikin tarihi sun taimaka wajen canja wa al’ummar duniya wuraren zama, wanda hakan kuma ya sanya Hausawa suka sake cudanya da wasu al’ummu da yanaye-yanaye mabambanta.
•    Ruwan dufana shi ne lokaci na farko da al’ummar Hausawa suka sake hayayyafa tattare da sauran al’umomin duniya a sassan duniya daban-daban. Mazaunin farko bayan ruwan dufana yana da dangantaka da yadda Hausawan yanzu suka kasance a cikin tsawon tarihi.
•    Shekara 185,000 da suka wuce kuma masana sun yi nuni da cewa, an bar labarin mutanen da, masu kama da birai, masu karamar kwakwalwa, masu karamin kai da tankwasasshe ko lankwasashen jiki, aka samar da mutum na zamani.
•    Mun riga mun kuma nuna cewa shi wannan mutum na zamani asalinsa bakar fata ne, daga cikinsa aka samar da sauran al’ummar duniya da muke gani a yanzu, Turawa ko Larabawa ko Asiyawa ko Astireliyawa ko Afirkawa ko Amurkawa, ciki kuwa har da Hausawa.
•    Mun kuma kara tabbatar da binciken masana da ya nuna cewa bakaken fatar da suka bar Afirka, suka nasa kwan da ya samar da al’ummar duniya baki daya, sun bar Afirka a tsawon shekaru, amma daga shekara 60,000 suka soma dawowa  Nahiyar Afirka, ciki har da kasar Hausa.
•    Dawowar da wadannan kakanni namu suka yi sun yi tsawon shekaru bisa hanya tun daga Nahiyar Asiya zuwa Nahiyar Larabawa da zaunuwa a yankin Afirka ta Arewa.
•    A daidai lokacin da wadannan kakani namu ke wanzuwa a yankin Afirka ta Arewa, musamman a Masar da Palasdinu da Parisa da Hijaz, sauran ’yan uwan Hausawa na can zaune a cikin dazuzzukan kasar Hausa, suna rayuwarsu ta yau da kullum, musamman ta arnanci, domin addini bai je gare su ba, sai na gargajiyar da suka gada.
•    Bincike ya kuma nuna cewa daga shekara 4,000 wasu daga cikin al’ummar wannan yanki na Arewacin Afirka da yankin Palasdinu da Parisa sun bar wannan yanki zuwa sassan kasar Hausa. Ana ganin wadannan al’umma dangogin Annabi Ibrahim ne da matarsa Saratu da Hajara da ’ya’yansu Is’hak da Isma’il.
•    Haka kuma daga baya an samu wasu daga cikin kabilu ko al’umomin da suka rayu da Annabi Musa sun warwatsu zuwa wasu sassan na kasar Hausa, wadanda suna cikin al’ummar da suka samar da wasu kasashen Hausa, musamman kasar Daura.
•    Daga nan kuma, musamman daga shekara ta 1,000 aka shigo da labarin zuwan baki a cikin tarihi da adabin bakan Hausawa, wanda kamar yadda muka nuna shi ne ya haifar da taririhin Bayajidda a kasar Hausa.
Daga wadannan hasashe-hasashe ne muka dawo ga kokarin neman daidaita tarihin kasar Hausa ta hanyar sanya tarihi ko labarin Bayajidda cikin kokon bincike don a ga yadda yake a zahiri, bisa wannan kokari mun fahimci abubuwa kamar haka:
•    An taba yin wani wai shi Bayajidda ko Abu Yazid, sai dai ba dan Sarkin Bagadaza ba ne, Babar ne daga Tunisiya, ya kuma rasu a shekarar 947, shekara 53 kafin bayyanar Bayajidda ko Abu Yazid a kasar Hausa.
•    Muka nuna cewa idan kuwa ba Bayajidda ko Abu Yazid ba ne ya zo kasar Hausa a lokacin, to, da alama wani daga cikin zuriyarsa ko dakarunsa ne suka kutso suka aza sarautun kasar Hausa.
•    Mun kuma kara jaddada cewa ko kafin wannan jini na Bayajidda ko Abu Yazid ya iso kasar Hausa ya zama ‘tushe’ ko ‘asalin’ kasashen, akwai kasashen da al’ummarta da suka hada da Daura da Gobir da Zazzau da Santolo da Kabbi da Pawwa, wadanda duk sun rayu da kafuwa da ginuwa kafin wani wai shi Bayajidda ko jininsa ko dakarensa ya taka kafa a kasar Hausa.
Daga karshe kiran da za mu yi, shi ne a sake nazari da bincike, fatarmu ita ce wannan tsokaci da muka yi na tsawon wata 4 ya kasance wata matattakala zuwa ga gano gaskiyar wannan lamari. Allah Shi ne Masani.
Mun kammala