✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (2)

Tambayar da za mu yi kokarin amsawa ita ce ko an taba yin wani wai shi Bayajidda? In an taba yi yaya aka yi ya…

Tambayar da za mu yi kokarin amsawa ita ce ko an taba yin wani wai shi Bayajidda? In an taba yi yaya aka yi ya zo kasar Hausa? Idan har ya leko, me ya sa ake cewa shi ne asalin kasashen da sun rayu, sun ginu, tun kafin a haife shi ko a haifi iyaye da kakanninsa? Haka kuma za mu yi kokarin fahimtar ta yaya wanda ya samu al’umma da kasashe ginannu za a ce shi ne ya samar da Hausa da Hausawa? Shin da gaske ne ya kashe wata macijiya ko maciji a wata rijiya ta Kusugu? Haka kuma shin da ya zo, ya yi aure a daular Bornu ko kasar Daura? Shin da gaske ne ya haifi ’ya’ya da jikokin da ake cewa su ne suka kafa kasashen da ake kira Hausa Bakwai da Banza Bakwai? Me ya sa kasar Kabbi da Zamfara za su kasance cikin Banza Bakwai, alhali a asali da ginuwa sun ma fi wasu daga cikin kasashen Hausa Bakwai kafuwa da tarihi? Shin gaskiya ne Bayajidda bai taka kasar Daura ba, balle ya hadu da wata Daurama?
Amsa wadannan tambayoyi yana bukatar nazari mai zurfi, saboda haka bari mu soma da bin diddigin yadda aka samar da wannan labari na Bayajidda da yadda ya ginu a cikin tunanin mutanen yankin kasar Hausa har ya zama abin tokabo ga al’ummar da wadanda suka zo cikinta a mabambanta zamunna.
Abin da da za mu kira asalin tarihihin Bayajidda da kuma yadda ya tsaru, ya ginu, ya kuma warwatsu tsakanin al’ummar kasar Hausa ya biyo matakai daban-daban cikin tarihi. Abu na farko dai shi ne tarihihin ya samu ne tsakanin mutanen kasar Hausa, abin ya faru ko bai faru ba, a yanzu ba shi ke da muhimmanci ba. Mun kuma sani su kuma yawancin Hausawa ba masu ilimin karatu da rubutu ba ne a tsawon tarihi sai da suka hadu da baki; Larabawa da Turawa. Saboda haka dukkan abin da Hausawa suka sani ko suka ankara da shi na daga tarihin al’ummar kasar Hausa ya samo asali ne daga abin da ake kira kunne ya girmi kaka. Abin da wani ya ji ne, wani ya karas, da gaskiya ko ba gaskiya, da karin gishiri ko ba karin gishiri. A irin wannan tanadin tarihi dole ne a samu wani bangare da ke dauke da abubuwan da ba su da tushe ko asali, saboda kwalwar dan Adam ba tabbatacciyar ma’adana ba ce.
bangare na biyu da ya samar da labarin ko tarihihin na Bayajidda shi ne zuwan baki kasar Hausa, musamman Larabawa, da yake sun zo da karatu da rubutu. Zuwan nasu ya taimaka wajen adana tunane-tunane da tarihe-tarihen al’umma da wannan yanki na kasar Hausa a rubuce cikin Larabci. Yawancin irin wadannan Larabawa da suka ziyarci kasar Hausa sun samu labarin al’ummar da yankin ne daga abin da ’yan yankin suka bayyana musu, su kuma suka nakalta, suka rubuce a takarda. Abin da ke da muhimmanci a nan shi ne, abin nan da al’ummar suka bayyana wa Larabawan da suka tako wankin yanki ba dole ya kasance gaskiya ba, domin masu bayyana labarin su ma ba komai suka rike ba a cikin kwalwarsu ba, haka kuma ba komai ne da ’yan kasar suka bayyana wa Larabawan farkon ba, su kuma Larabawan suka kattaba shi kamar yadda suka ji shi ba, wato na gaskiya ko mai karin gishiri.
Hanya ta uku da aka gina wannan labari ko tarihihi na Bayajidda ita ce ta hannun manyan malamai da masana ’yan kasar Hausa da suka samu ilimin addinin Musulunci, suka kuma nakalci Larabci, musamman masu jihadi da mukarrabansu, sa’annan daga baya suka karanci abubuwan da Larabawan farko suka kattaba a littattafansu da kuma tambayar tsofaffi da ma’adana tarihi game da tarihin yankin kasar Hausa da al’ummar wannan yanki, suka sake rubuta tarihin a cikin littattafansu.
Fasali na hudu da za mu iya kawowa na samuwa da ginuwar wannan labari ko tarihihi na Bayajidda shi ne wanda Turawan da suka leko kasar Hausa suka samar a littattafansu. Kamar yadda ya faru kafin zuwan nasu, an dai riga an samar da tarihihin a rubuce a cikin Larabci. Saboda haka koda  wadannan Turawa suka zo a matakai mabambanta; wato ’yan leken asiri da sanin labarin kasa; ko wadanda suka zo cinikin bayi;  ko kuma Turawan Mishan da na mulkin mallaka; sun ci karo da labaran kasar Hausa da al’ummomin da ke cikinta tattare a wuri daya a rubuce ko a cikin kwakwalwar ’yan kasa. Sun kuma zauna sun rubuce labarin ko tarihihin daga abin da kodai sun ji daga bakunan mutanen kasar Hausar ko kuma sun karanto a littattafan Larabawan farko da suka zo kasar Hausar ko kuma sun karanto daga littattafan malaman kasar Hausar da kuma ayyukan masu jihadi. Kamar kullum abin da Turawan nan suka tanada a cikin littattafansu, ba dole ne ya kasance gaskiya ba, domin kuwa inda suka samo labarin ko tarihihin mun riga mun fahimci cewa yana da nakasu, ke nan abin da suka tanada, shi ma zai kasance da nakasu.
A halin yanzu ba wani aikin Larabawan farko da za a iya kawowa da ke dauke da wannan labari ko tarihihi na Bayajidda kai-tsaye da kuma yadda ya zo kasar Hausa, amma an samu cikakken labarin daga mahanga akalla guda hudu. Mahanga ta farko ita ce wadda har yanzu ake yawo da watsa ta ta kunne ya girmi kaka, wato wadda duk yaron da ka tambaya a da ko kuma a yanzu zai iya kawo maka ita da ka, wato ta wani da ake cewa bai jin Hausa da, ya zo ya auri Sarauniya Daurama. Duk inda ka shiga cikin kasar Hausa, musamman yankin Daura da Katsina da Kano za a iya bayyana maka wannan tarihihi; musamman a Daura tun da ba wani rubutaccen al’amari da ya zo da shi kafin zuwan Larabawa.
Rubutaccen tarihihin na Bayajidda na farko da masana suka bayyana an gani shi ne wanda Muhammadu Bello dan Shehu Usmanu danfodiyo ya zo da shi a cikin littafinsa In fakal-maisur fi ta’rikh biladil-takrur. Wani bangare na wannan littafi shi ne wasu Turawan leken asiri da neman labarin kasa, wato Denham da Clapperton, suka debo suka fassara daga Larabci suka buga a cikin littafinsu a shekarar 1826. Daga wannan littafi ne ake jin Turawa suka fara cin karo da tarihihin Bayajidda a rubuce, inda aka yi maganar kasar Katsina da Kano da Zariya da Daura da Rano da ‘Yareem’, wadanda aka ce dukkansu ’ya’yan wani bawa ne na Sultan na daular Bornu wai shi Bawo.

Za mu ci gaba