✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (3)

Kamar yadda muka gani a baya idan ana maganar labarin Bayajidda a rubuce, ana iya cewa ba a ci karo da wani abu ba sai…

Kamar yadda muka gani a baya idan ana maganar labarin Bayajidda a rubuce, ana iya cewa ba a ci karo da wani abu ba sai daga dan abin da Muhammadu Bello dan Shehu Usmanu danfodiyo ya zo da shi a cikin littafinsa Infakul-Maisur Fi Tarikh Biladil-Tukrur. Wani bangare na wannan littafi shi ne wasu Turawan leken asiri da neman labarin kasa, wato Denham da Clapperton, suka debo suka fassara daga Larabci suka buga a cikin littafinsu a 1826. Kamar yadda masana suka yi nuni daga wannan littafi ne (na Muhammadu Bello) ake jin Turawa suka fara cin karo da tarihihin Bayajidda ko wani abu mai kama da shi a rubuce, inda aka yi maganar kasar Katsina da Kano da Zariya da Daura da Rano da ‘Yareem’, wadanda aka ce dukkansu ’ya’yan wani bawa ne na Sultan na Daular Bornu wai shi Bawo.
Duk da cewa ba inda Muhammadu Bello ya kawo batun Bayajidda ko Abu Yazid karara a cikin littafinsa, wanda ke nuna mana rashin ingancin labarin tun a wancan lokaci, za a iya danganta wannan tsakure na Bawo da tarihihin Bayajidda, kamar yadda ya zo daga baya, domin an nuna cewa shi Bawo da ne ga wani wai shi Bayajidda da aka haifa da sarauniya Daurama. Amma har yau babu tabbacin wannan hasashe shi ma, domin shi kansa Bawon kamar yadda wasu masanan suka yi nuni, bai da alaka da Daura ko Daurama balle kuma Bayajidda. Danganta shi da bauta da kuma Borno da Muhammadu Bello ya yi wai an yi haka ne domin a nakasa mulkin sarakunan kasar Hausa  don jaddada jihadin da su danfodiyo suka yi, kamar yadda wasu masanan, musamman Turawa suka yi nuni wanda da alama bai da mazauni na bincike, domin kuwa hujjojin da ke zube a gaban masu jihadi da sauran al’ummomin kasar Hausa da kewaye a lokacin ya isa a jaddada addinin Musuluncin ba sai an danganta sarakunan Hausa da bauta ba, don a yake su.
Ba ma wannan kadai ba, da yake shi kansa Bawo ana da tababar sa hannunsa wajen ginuwa da tabbatuwar kasar Hausa, abin da ya dace a yi shi ne, a koma ga ainihin tarihihin na Abu Yazid ko Bayajidda a ga yadda batun ya shigo cikin tarihin kafuwar kasar Hausa da Hausawa.
Da yake farkon zuwan Turawa kasar Hausa abin da suka fi maida hankali a kai shi ne tattara da nazarin rayuwar Hausa da Hausawa ta fuskar amfani da tarihi da labarai da ayyukan adabi da suka ko dai tsinta a cikin littattafan Larabawan da suka riga su shigowa cikin kasar ko kuma daga abubuwan da suka ji daga bakunan ’yan kasa da suka ci karo da su ya nuna mana cewa akwai jita-jita cikin harkar.
Sai dai kamar yadda na nuna tun da farko, ban da bayanin da Denham da Clapperton suka yi a cikin littafinsu na 1826, ba wani wuri kuma da aka taba ganin wannan tarihihi na Bayajidda ko Abu Yazid a rubuce. Denham da Clapperton (1825-1827) da Henrich Barth (1850-1855) da Charles Henry Robinson (1893-1896) dukkansu ba wanda ya tattaro wannan rayuwa ko labarin ko kuma tarihihin a cikin daruruwan ayyukan da suka ci karo da su a wasu sassa na kasar Hausa.
Saboda haka an soma cin karo da wannan tarihihi ne a cikin karikitan Frank Edgar wadanda ya tattara a zamansa na Sakkwato da zagayensa zuwa wasu sassa na kasar Hausa. Wadannan karikitai suna nan jibge a dakin ajiyar taskokin tarihi da ke Kaduna tun shekarun 1950. Daga cikinsu shi Frank Edgar ya wallafa ayyukansa na Litafi na Tatsuniyoyi na Hausa da aka buga a tsakanin 1911-1913. A cikin wannan littafi ne aka zo da tarihihin Bayajidda a karo na farko har iri uku, masu mabambantan kamannu. Da yake Frank Edgar ya zo da su a matsayin tatsuniya a cikin littafin tatsuniyoyi da alama ya dauke su a matsayin haka, ko kuma dai wadanda suka ba shi labarin suka bayyana masa su a matsayin tatsuniya a maimakon tarihi na gaskiya. Ko ma dai mene ne gaskiyar lamarin, nan ne aka fara cin karo da tarihihin Bayajidda ko Abu Yazid a rubuce.
Bayan wannan bayani da aka gani a rubuce game da tarihihinn Bayajida da Abu Yazid na Frank Edgar, akwai wadansu irinsu da Rattary (1913) da wasu Turawan mulkin mallaka irinsa suka kattaba daga ayyukan wasu Turawan da bakunan wasu Hausawan da suka rayu a wasu zanguna na kasar Hausa. Abin da ya sa ba a faye mayar da hankali kansu ba, sai ganin cewa suna dauke da bayanin da ke cikin na Edgar ko kuma daga baya wanda aka tsinta a cikin tarihin kafuwar Kano.
Sai dai wanda ya yi tashe, ya samu karbuwa shi ne na Herbert Richmond Palmer wanda aka nada Mataimakin Razdan na Lardin Arewa a 1904, ya zama Razdan a 1905 a Katsina, wadda a lokacin ke hade har da Daura. Shi ne ya sake tsarin mulkin Lardin Katsina da sake shata iyakoki da samar da sababbin yankunan hakimai da dagatai, shi ne kuma ya dora Sarkin Katsina Muhammadu Dikko a kan karagar mulki a 1906.
Ke nan idan aka ce Palmer shi ne asasin gina Lardunan Arewacin Najeriya a wancan lokaci da alama ba a shara ta ba. Bincike ya nuna cewa tun daga 1906 har zuwa 1911 ya sa hannu wajen tsara mulkin sarakunan Arewa ta fuskoki da dama. Daga1915 zuwa 1916 yana Kano a matsayin Mukaddashin Razdan, a 1917 aka yi masa Razdan na Borno. Zaman da Palmer ya yi a Katsina (da Daura) da Kano da Borno ya ba shi damar nazartar al’adu da harsuna da adabi da kuma rayuwar al’ummar wadannan yankuna. Wasu masana na ganin cewa wannan dama ce ya yi amfani da ita wajen nazari da nakaltar yanayin kasar Hausa da tarihinta. Ya dai iya Hausa da Fillanci da Kanuri da Larabci gwargwado, shi ya sa ma wasu masana ke nuni da cewa shi masanin kasar Hausa da Hausawa ne a cikin tarihi.
Bincike ya nuna cewa Palmer matafiyi ne domin bukatar nazari da bincike, domin ya fahimci al’ummar da yake mulki ya ratsa kasashen yankin Sudan daga 1918, inda ya bar Borno zuwa Wadai da Dafur har Sudan. Shi ne ya assasa kafuwar Kwalejin Horar da Malamai ta Katsina a 1922 a lokacin da yake Mataimakin Gwamnan Arewacin Najeriya daga baya cikakken Gwamnan Arewacin Najeriya a 1925.
Bincike ya nuna cewa Palmer ya yi kusan shekara 26 ana damawa da shi a cikin mulkin Arewacin Najeriya, kuma a cikin wannan tsawon gwagwarmaya ne ya natsu domin sake fasalin tarihin Hausa da Hausawa da Fulani da Kanuri da ke yankin kasar Hausa. A shekarun da ya yi na bincike ne ya rubuta littafinsa da ya lakaba wa suna da Sudanese Memoirs, wanda aka buga a 1928.
Shi wannan littafi na Palmer shi ne ke dauke da tarihihin Bayajidda karo na biyar a rubuce, wanda masana ke nuni da tarihihin Bayajidda mai alaka da Daular Borno. A cikin wannan tarihihi ne kuma aka ga shigowar Abu Yazid da barin kasar Borno da ya yi da Gimbiya Magira, inda bayan wani ‘lokaci mutanen Borno suka samu labarin cewa Abu Yazid ya zama Sultan na Daura.’
Shin shi wannan Abu Yazid da ya zama Sarkin Daura a shekara ta 1,000 da muka gani a cikin littafin Palmer da aka buga a 1928, shi ne kuma aka ce ya mutu a shekarar 947 (shekara 53 kafin zuwan Bayajidda kasar Hausa) a cikin littafin Palmer a shekarar 1936? Yaya batun yake ne?
 
Za mu ci gaba