✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (4)

Ga alama dai shi Palmer da ya kawo labaran biyu na Bayajidda ko Abu Yazid a littattafansa na shekarar 1928 da kuma 1936 akwai abin…

Ga alama dai shi Palmer da ya kawo labaran biyu na Bayajidda ko Abu Yazid a littattafansa na shekarar 1928 da kuma 1936 akwai abin da ke cikin tunaninsa ko kuma wadanda yake wa aiki, shi ya sa ya daburta lamurran. Bai yiwuwa a ce a littafinsa na farko Sudanese Memoirs ya ce Bayajidda ko Abu Yazid ya zo kasar Borno da Daura, a littafi na biyu kuma ya ce Bayajidda ko Abu Yazid ya rasu tun kafin ya zo kasar Hausa. Ko ma dai mene ne, bincike ne kadai zai kara mana hasken kan wannan batun.
Abin da za mu yi a nan shi ne mu tsakuro shin me Palmer ya ce game da wannan dan taliki Bayajidda ko Abii Yazid a cikin littafin nasa na biyu domin fahimtar yadda batu yake a zahiri. Ta yaya kuma abin da ya faru da shi wannan dan taliki ya shafi yankin Bornu da Daura bayan ya rasu, in da gaske ne abin ya faru a tarihi? Za mu takaita bayanin ne domin a ga irin yadda tunanin ya kasance.
Kamar yadda Palmer ya bayyana, ba wani ba ne Bayajidda ko Abii Yazid sai wani da aka ce Babar ne daga Arewacin Afirka, cikakken sunansa wai Abii Yazid Makhlad ibn Kaidad al –Zanati. An haife shi a shekarar 884; sai dai ba a da masaniyar takamaimai inda aka haife shi, an ce ko dai a birnin Gao ne ko kuma a kusa da birnin na Gao, wato a Tademekket, inda mahaifinsa a lokacin yake hada-hadar kasuwancinsa.
Mahaifin Abii Yazid an ce mashahurin dan kasuwa ne na gani-da-fada, dan kabilar Babar ne na al’ummar Zanata da ke cikin yankin Kudancin kasar Tunisiya ta yau, inda nan Abii Yazid ya girma, ya kuma tasa bayan haihuwarsa.
A shekarar 909 Miladiyya, wani da ake ce da shi ‘Ubaid Allah shi ya zama Kalifan Fatimawa na yankin Arewacin Afirka, a cikin tsawon shekara 24 da ya yi yana mulki, ya sha samun adawa daga sassa daban-daban na al’ummar yankin, ciki kuwa har da na wasu daga al’ummar Babar da Abii Yazid ke wa shugabanci, wato Ibadawa, da ke zaune a tsakanin al’ummar Jabal Awras. An ce in bacin irin yadda Kalifa ‘Ubaid Allah ya tashi tsaye, ya kuma tura sojoji suka dinga fafatawa da wadannan ‘yan adawa da mulkinsa bai kai labari ba. Matsi da kisan su da ya yi ta yi, ya sa wasu daga cikin su suka gudu, wasu suka famtsama zuwa sassan Makka da Madina, ciki kuwa har da shi Abii Yazid.
Bayan shekaru an ce a shekarar 937 Abii Yazid ya sake komowa Arewacin Afirka, ya sake sajewa da dakarunsa, a lokacin nan kuma wanda ke mulkin Fatimawa shi ne Al-ka’im, wanda ya gaji ‘Ubaid Allah a matsayin Kalifa. Sun sake fafatawa da dakarun Abii Yazid har Allah ya ba Kalifan sa’a dakarunsa suka kame Abii Yazid a garin Tuzur, amma an ce wasu daga cikin ‘ya’yansa da magoya baya sun bi hanyoyin da suka ci sa’a aka sako shi daga dauri. Daga wannan lokaci ne aka ce yakin basasa ya ta’azzara a Arewacin Afirka, har ‘yan adawa suka yi nasarar kame garin kairawan a shekarar 943, suka kuma yi fata-fata da sojojin Fatimawa da ke zaune a Al-Akhawan. Wannan nasara ita ta sa boren dakarun Abii Yazid ya kara ci gaba, sa’annan a daidai wannan lokaci aka ce boren Mahadi ya ta’azzara, sa’annan Kalifa al-ka’im a daidai wannan lokaci shi ma ya rasu, mulki ya koma hannun dansa al-Mansiir.
Hawan al-Mansiir ke da wuya abubuwa suka canza a fagen yaki da bore, shi kuma Abii Yazid daga shekarar 946 ya shiga kai hare-hare zuwa sassa daban-daban na yankin Arewacin Afirka da suka hada da yankin Susa, amma dakarun al-Mansiir sun fatattake shi, da shi da mayakansa, inda aka ce ya arce zuwa cikin hamadar Sahara; duk da haka  sojojin Kalifan ba su kyale shi ba, sun bi su da yaki har zuwa shekarar 947, inda suka tare shi, suka ci sa’a suka kashe shi a wani gari da ake ce da shi Kiyana, a yankin Zab, inda aka ce an babbaka gawarsa, aka saka cikin wani keji da wasu birai ke wasa da ita.
Sai dai a kula, kamar yadda rahoton binciken ya nuna, rasuwar Abii Yazid, ba ta sa an daina boren da Ibadawa suka soma ba, musamman daga ‘yan kabilar Babar da kuma ‘ya’yan Abii Yazid da suka ci gaba daga inda ya tsaya. Amma da yake abin nan da Hausawa ke cewa sarkin yawa ya fi sarkin karfi, ga kuma karfin hukuma, dole ta sa wadanda suka rage daga dakarun Ibadawa suka antaya cikin rairayin hamada, suka yi kudu, suka kuma bace daga tarihin Arewacin Afirka.
Daga dan wannan takaitaccen bayani za a fahimci abubuwa guda biyu muhimmai; na farko dai in har an yi Abii Yazid to da alama bai rayu ba, balle har ya shigo cikin kasar Bornu, ya wuce Daura. Abu na biyu kuma shi ne, in har lallai shi wannan Abii Yazid ya rayu, ya kuma iso kasar Borno da Daura, to da alama ba shi ba ne ya shigo cikin wannan yanki, saboda tarihihin shigowarsa kasar Hausa bai bayyana cewa shi Babar ba ne, a dukkan taririhin da aka gani a baya (cikin littafin tatsuniyoyi na Frank Edgar da na cikin tarihin sarautun Kano da na Sudanese Memoirs) ba inda aka bayyana haka, hasali ma sun fi mayar da hankali wajen cewa shi dan sarkin Bagadaza ne a kasashen Larabawa ba wai dan asalin Arewacin Afirka ba. Ta yaya za a tabbatar da haka? A cikin bayanan da muka yi a baya, mun ga yadda a rubutun Palmer ne kurum na 1928, ya gutsere labarin Bayajidda da cewa daga karshe mutanen Bornu sun sami labarin cewa Abu Yazid ya zama Sultan na Bornu. Ba inda Palmer ya zo da bayanin shigar Abii Yazid kasar Daura da yadda ya kashe macijiya har ya zama Sarki kamar yadda sauran suka yi, sai dai a littafinsa na 1936, inda da alama ya bi sahun sauran marubuta irin wannan tarihihi ne da suka riga suka kama kasa, shi ma ya cika nasa da labarin zuwan Abii Yazid kasar Daura daga Borno da kashe maciyar da ya yi.
Duk wannan ba shi ne matsalar wannan tarihihi ba, babbar matsalar ita ce, shin Abii Yazid Balarabe ne ko Babar? Shin mutumin Bagadaza ne ko yankin kasar Tunisiya?  Shin ya zo kasar Hausa ko kuwa dai shara ta aka yi?
 Za Mu Ci Gaba.