✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (7)

Saboda haka batun da ya dace mu zauna kansa shi ne, wani daga cikin iyalai ko dakarun Abii Yazid shi ne Bayajidda, ba ainihin mataccen…

Saboda haka batun da ya dace mu zauna kansa shi ne, wani daga cikin iyalai ko dakarun Abii Yazid shi ne Bayajidda, ba ainihin mataccen da aka baro can baya da dadewa ba. In kuwa haka ne, me za mu ce game da takobin Gaya da kashe macijiya da auren Kuyanga da Sarauniya Daurama, su ma sun auku?
Ba mai iya tabbatarwa ko kuma karyata irin wannan batun kai tsaye. Abin da bincike ya nuna shi ne daga cikin ‘ya’ya ko jikokin Abii Yazid ko kuma dakarun nasa wasu sun shigo cikin wancan yanki na Bornu zuwa Biram da Gaya da kuma Daura daga shekarar 948 bayan rasuwar Abii Yazid din. Wadannan iyalai ko dakaru daga baya sun saje da al’ummar da suka iske, ciki kuwa har da yankin Daura. Ana kuma jin wadannan iyalai na Abi Yazid su ne suka tsara sabon yanayin mulki a wannan yanki wanda ya samar da kasar Hausa kamar yadda za mu gani nan gaba.
Abin kara lura a nan shi ne a daidai wannan lokaci da iyalan Abii Yazid ke shiga da fici a wannan yanki, Daular Bornu tana cikin yanayin rayuwa irin ta Fulani, al’ummar yankin na kekkkebe, zazzaune a sassa daban-daban, suna kuma gudanar da mulki bisa tsari irin nasu. A kuma lura idan ana maganar Bornu, ba wai yankin jihar Borno da muke gani a yau ba ne a Arewacin Nijeriya, ta wuce nan, har ta shiga cikin yankin Chadi da sassan Arewacin Afirka kamar yadda muka gani can baya. Sai dai ita Daular Bornu ce ta samar da Bornon da muke gani a yanzu. Ana jin kuma zuwan ‘ya’ya da jikoki ko dakarun Abii Yazid ya sanya wurin ya daidaitu da tsarin sarauta irin na zamani.
Dangane da haka muna iya cewa garuruwan Biram da Gaya da Daura da sauran makwabtan yankin nata suna cikin wadannan al’ummomi da suke rakube da tsohuwar Daular Bornu, shi ya sa ma wasu ke ganin cewa dukkan abin da ya faru bayan rasuwar Abii Yazid da shigowar dakarunsa wannan yanki tatsuniya ce da aka gina daga cikin tarihin wani abu da ya taba faruwa can baya.
Wannan tunani shi ne yawancin masana suka zaunu kansa. Akwai cikin masana da ke ganin cewa ai da wannan tatsuniyar ce ma aka gina tarihihin Abii Yazid ko Bayajidda da asalin Hausawa. Ga abin da wani dan yankin, wato Imam Umaru ya bayyana ya faru a wannan lokaci; ya ce wai an ce akwai wadansu maharba guda biyu da ke zaune a wannan yanki da ake ce da shi Gabi da iyalansu da dakarunsu, an ce ita Daura diyar karamin cikin su ce, wadda aka sa wa suna Fatima ko kuma Dauratu. An ce wai ba ta jin wani yare har sai da mahaifiyyarta ta rasu, wanda ya sa wai suka ce da abin da take fada da ‘haza kalamu Hausa’ cikin Larabci, wanda matafiyin nan Imam Umaru ya ce shi ne asalin kalmar Hausa da kuma samuwar Daura da Daurama, domin harshen da ta yi magana da shi, ba Larabci ba ne, ba kuma Kanuri ko Tamashek ba ne.
Kamar yadda bayanan masu bincike suka nuna ita Dauratu, ita ce ta girma ta gaji gidansu, ta zama jaruma, har ta kasance ba ta hulda da maza don ta fi karfinsu, daga baya wani daga cikin dakaru, kuma bawan Mai na Bornu da ya yi rashin kirki, Mai din zai kashe shi, ya gudu (kila kafin ya isa kasar Dauratu ya tsaya a Biram da Gaya, inda ya sami takobi) daga baya ya isa kasar Dauratu, ya nemi ya aure ta, ta ki, ta aura masa kuyanga, wadda ta haifi da namiji. Ta haka ta dinga wulakanta Dauratu saboda shi, ko magana aka yi mata sai ta ce ‘Wo’, a wulakance. Wannan ya bata wa Dauratu rai, daga baya ta yi kwalliya irin ta mata, ta kwanta da wannan bawa, ta sami da namiji ita ma, ta sa masa suna ‘Ba Wo’, wato ba Wo kuma, wato ba sauran wulakanci.
Wannan tarihihi ba abin da ya yi sai kara sanya tababa game da Dauratu da kasar Daura, domin dai tun da farko an nuna cewa ita sunanta Fatima, amma kuma ba ta jin Larabci ko Kanuri ko Tamashek, ke nan dai Musulma ce, ko gidan nasu Musulmi ne, wanda ga dukkan alamu da wuya ya kasance haka, duk kuwa da cewa iyalan Abii Yazid Musulmi ne kamar yadda muka gani tun farko. Ke nan idan an biye wa wannan labari na Imam Umaru, za a ga ba wadansu cikakkun bayanai da muka gani dangane da kasar ta Daura da Biram da Gaya kamar yadda ya zo a cikin tarihihin da muka gani na Sarauniya Daurama tun can asali. Abin da yake muhimmanci a nan shi ne dai an yi kasar Daurar da Dauratu ko Daurama wani abu makamancin haka. Yanayin aurenta da samuwar ‘ya’yan nata ne ke da shigewa duhu.
Bayan kasar Daura da Dauratu ko Daurama, abu na biyu da ke da muhimmanci a cikin wannan tarihihi shi ne na rijiyar Kusugu da yadda ta yi tasiri a rayuwar al’ummar wannan yanki. A tuna fa duk inda rijiya ta kasance abin tokabo, to abu daya zai nuna mana a nan, akwai matsalar ruwa a yankin da kasar Daura ta samu kanta. Wannan haka yake, domin kuwa tarihin yankin ya nuna cewa busasshiyar kasa ce, ta hamada, ruwa na da matsalar samuwa, shi ya sanya duk inda aka samu rijiya, to wurin kan zama matattarar mutane, domin rayuwa. Idan muka amince da wannan tunanin za mu iya cewa lallai rijiyoyi a wannan yanki tun daga Yammacin Chadi har zuwa cikin Daular Bornu da yankin Daura ba su da yawa sosai, saboda haka samun rijiya ko matattarar ruwa a Daura abin jin dadi ne ga al’ummar yankin.
Abin da kila ba za a iya amincewa da shi ba shi ne a ce macijiya ta hana al’ummar wannan yanki dibar ruwa daga cikin rijiya sai mako-mako. Abubuwa uku za su sa a ki amincewa da haka. Na farko dai garin na Daura dakaru, jarumai, maharba ne suka samar da shi, bai yiwuwa a ce macijiya ta hana dibar ruwa a rijiya da ke da muhimmmanci ga rayuwar al’ummar. Na biyu, an yi nuni da cewa ita kan ta Saurauniyar sunanta Fatima, kila Musulmi ne ke nan, da wuya kuwa Musulmin kwarai su amince da tsibbu ko tsafi irin wannan. Abu na uku, shi kan sa tadi irin na macijiya abu ne da ya dade cikin tarihi da labaran wannan yanki, amma an fi dora shi bisa bauta irin ta gumaka ko arnanci ba dai Musulunci ba. Ke nan al’ummar Daurar arna ne, ko masu bautar gumaka.

Za Mu Ci Gaba