✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hausa Da Hausawa: Wane ne kuma Bayajidda? (9)

Idan ba su, to, yaya aka yi aka samar da kasashen da muke tokabo da su a yau a matsayin Hausa Bakwai ko Banza Bakwai,…

Idan ba su, to, yaya aka yi aka samar da kasashen da muke tokabo da su a yau a matsayin Hausa Bakwai ko Banza Bakwai, musamman idan muka yi la’akari da cewa Bagauda da aka ce ya kafa Kano ko kafin ya zo ya iske akwai marayar Santolo, wadda ita ce birnin ba Kanon ba, haka kuma koda ya zo ya girbi sashen da ya dasa nasa sabon birnin na Kano, ai akwai Kanon a gindin Dutsen Dala, inda masana suka yi nuni da cewa nan ne ma Kanon ya rayu, wurinsa ne ake zuwa a bakin dutsen, shi ya haifar da kiran wurin da Kano. Ke nan Bagauda ba shi ne asalin Kano ba, ba kuma dan Bawo ba ne ko jikan Bayajidda, wani dakaren ne can daban, kila daga cikin dakaru ko ’ya’yan Bayajidda ko Abu Yazid da muka yi bayani can baya! Me ya sa muka ce haka? Ko a cikin Tarihin Sarakunan Kano da ake bayanin Bagauda cewa aka yi a daidai shekara ta 1,000 Bagauda ya yi zama a wani gari da ake kira Adirani har tsawon shekara biyu, daga nan ya wuce zuwa wani gari da ake ce da shi Barka, nan ma kusan shekara biyu daga can sai garin Sheme a kasar Kazaure, inda daga can ne ya isa Kano, inda ko dai shi ko danginsa suka mulki Kano na kusan tsawon shekara 60. Tambayar da za a iya yi ita ce, shin ana haihuwarsa ne ya bar gida don mulkin wadannan kasashe?
Ko kuwa dai sai da aka dauki tsawon lokaci? An yi wannan tambaya ne ganin cewa yawancin tarihe-tarihen da ake da su game da Abu Yazid ko Bayajidda da zuwansa kasar Daura daga shekara ta 1,000 ko 1,100 suka fara. Da yake kuma ba wani takamaiman lokaci ko rana ko wata ko kuma shekara da aka nuna cewa sun iso kasar Hausa ko Daura, ba mai iya cewa ga daidai lokacin da aka haife su ko yadda suka girma har suka fice daga Daura ko Biram domin zama asasin Hausa Bakwai da Banza Bakwai. Abin da muka riga muka ayyana tun can baya daga nazarce-nazarcen masana shi ne, wanda ake kira Abu Yazid ko Bayajidda ya dai rasu tun a shekarar 947, saboda haka shekara 53 ko 153 ke nan iyalansa ko dakarunsa suka yi bisa hanya kafin su shigo Daura, idan har sun shigo din, har aka yi aure da Daurama akalla ana neman shekara kafin a haihu, idan kuma an haihu (wato su Karba-Gari da Bawo), ana bukatar a girma, a zama mutane kafin a hau kan gadon sarauta. Idan mun dauki shekarun girma daga 16 zuwa sama, ke nan akalla ’ya’yan za su kasance ’yan shekara 18 kafin su yi aure da haihuwa da hawan gadon sarauta. An ce Bawo ya haifi ’ya’yan nasa su shida (duk da ba mu san wane ne na farko ba) cikinsu akwai Bagauda, akalla shi ma zai yi shekara 18 kafin ya fita watangaririya zuwa wasu sassa na duniya. Idan kuma muka bi tafiye-tafiyen Bagauda zuwa Adirani da Barka da Sheme, inda akalla ya yi shekara 6, a daidai lokacin da ya isa Kano yana da shekara 24 ke nan. A nan kuma shi da iyalansa da magada sun yi mulkin shekara 60, za mu ce ke nan daga shekara ta 1,000 ko 1,100 zuwa karshen mulkin Bagauda a Kano, an samu shekara 102. Ke nan idan tarihin daidai ne, karshen mulkin Bagauda a Kano zai kama a shekara ta 1102 ko1202, wanda daga dukkan bincike ba hakan ba ne.
Mun dauki wannan dogon lokaci muna bin wannan tarihi da kuma tattace duk wani bayani domin mu kara tabbatar da rashin ingancin wannan taririhi, duk da cewa mun ce ana iya samun kanshin gaskiya a cikin taririhin, amma ba wani bincike da ya nuna cewa Abu Yazid ko Bayajidda ne ya zo kasar Hausa ya auri Daurama. Ke nan akwai tababa ga dukkan bayanan da ke tattare da taririhin.
Saboda haka abin da za mu yi shi ne, mu bi tarihin wadanda suka kasance ginshikan wannan tarihihi, mu ga shin su din ma sun kasance gaskiya ko kuwa dai abin da aka saba fada ne na kunne-ya-girmi-kaka, wanda yawanci bai zama gaskiya?
Mu soma da ita Daurama, bayanai da binciken masana sun nuna cewa ita kanta ba ta da tarihin asali. Wasu masu bincike sun ce sunanta na asali Fatima, ke nan Musulma ce, amma kuma daga irin yadda bayanai suka zo game da ita, bai yiwuwa a ce Musulma ce, domin kuwa al’adun da ake a kasar Daura a zamaninta ba na Musulunci ba ne. An kuma ce wai a lokacin da aka haife ta ba ta jin Larabci ko Tamashek, haka ta girma, shi ya sa ma wasu daga cikin mutanen kasar suka ce ai ba ta jin Hausa cikin Larabci, wai daga nan aka samu harshen Hausa, wannan ma bai iya zama gaskiya, domin da Larabci mutanen nata suka yi magana, ita me ya hana ta iya Larabcin? Haka kuma wasu masana sun ce ai sunanta na asali shi ne Dauratu, kuma’yar maharba ce, wadda ta nakalci tsafe-tsafe, ke nan Fatima ba ita ce Dauratu ba, domin tsafi bai tafiya da Musulunci. Wasu masanan ma cewa suka yi ai ita da kanta zuwa aka yi da ita Daura, domin baiwar sarakunan Daular Bornu ce, sayo ta aka yi, aka zo da ita Daura, har ta zama wata jaruma ta mulki jama’ar kasar. Ke nan ba abin da ya hada ta da sauran Daurama 9 da aka yi kafin zuwanta, kila su ma duk baki ne.
Idan kuma muka koma ga shi kansa Karba-Gari dan kuyangar Daurama, za a ga cewa shi ma dai bai da cikakken asali, wasu na cewa ai bawan Bornu ne shi ma, wasu suka ce ai Bakibde ne, wasu kuma suka ce ba a ma yi shi ba, shaci-fadi ne. Shi kuwa Bawo dan Daurama, daga sunansa aka fara samun tababa na ko shi ma da ne ba bawa ba. Wasu masana sun ce ai sunan nasa daga Bawa ne, ke nan bawan mutanen Bornu ne shi ma, kamar ita Daurama. Wasu suka ce ai shi ma Bakibde ne daga Masar, wasu kuma suka danganta shi da kabilar Barbar na Arewacin Afirka. Daga binciken masana, ba wani da ya ce haihuwarsa aka yi Daura kamar yadda tarihihin Bayajidda ya nuna, sai dai a ce zuwa ya yi da girmansa.
Shi kuwa Bagauda da aka ce ya sari sabon birnin Kano, shi ma an nuna cewa zuwa ya yi da girmansa, kuma sunan Bagauda lakabi ne, ba sunan yanka ba, shi ya sa wasu ke ce da shi Bagoda, ko kuma Bakibde, wato mutumin kasar Masar ne shi ma, da girmansa ya zagaye kasashen Hausar da muka yi bayani, ba kuma jinin Daurama ba ne ko wani mijinta da ake ta yayatawa.
Idan kuwa haka tarihin wadannan mutane da suke da gurbi a cikin tarihin kasar Daura da wasu daga cikin kasashen Hausa ya kasance cikin tababa da taraddadin tunani, ke nan akwai bukatar mu canja akalar bincike zuwa ga neman asali irin na gaskiya, kuma daga dukkan alamu zaren tunanin ne ya tsinke, domin binciken da ake gani na da inganci, shi ne wanda ke nuna cewa al’ummar Daura da wasu sassan kasar Hausa suna daga cikin kabilun nan 40 na Yahudawa da suka yi makuwa a lokacin da suka bar Masar zamanin Fir’auna, wasu daga cikinsu ne asalin Hausawa ko mutanen Daura. Shin wannan shi ne gaskiyar lamarin?
 Za mu ci gaba