✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hawwa Suntai: Makomar siyasar Jihar Taraba

Duk ta gefen da ka hango al’amurran da ke gudana a Jihar Taraba, zai yi wuya ka tsallake matar gwamna, Misis Hawwa danbaba Suntai, domin…

Uwargida Hawwa Danbaba SuntaiDuk ta gefen da ka hango al’amurran da ke gudana a Jihar Taraba, zai yi wuya ka tsallake matar gwamna, Misis Hawwa danbaba Suntai, domin yadda abubuwa suke gudana a jihar, ba za a yi ba tare da ita ba.  
Kafin hadarin jirgin saman da ya auku ranar 25 ga watan Oktoba na shekarar 2012, Misis Hawwa ita ce kashin bayan dukan nasarorin da mijinta Gwamna Suntai ya samu a Jihar Taraba. Masu lura da harkokin yau da kullum a fagen gudanarwa, sun yi amanna cewa ta yi ruwa, ta yi tsaki wajen shiga gaba don ganin mijin nata ya kai gaci domin tun a shekarar 2007 lokacin da aka tabbatar da takarar danbaba Suntai, bayan da aka soke ta danladi baido, sai ta yi damarar yakin neman zabe.
Tare da hadin guiwar Misis Priscilla Nyame, matar tsohon gwamnan jihar, Rabaran Jolly Tanko Nyame, Hawwa Suntai ta karade dukan kananan hukumomin jihar 16 tana hada kan mata, musamman da sauran jama’a don su goyi bayan maigidanta, a karkashin matashiyar cigaba da ayyukan da Jolly Nyame ya faro.
Yayin da aka rantsar da Gwamna Suntai, Hawwa kuma ta dare kujera Matar Gwamna, sai ta cigaba da abin da matar tsohon gwamnan ta fara na bunkasa Cibiyar Bunkasa Mata da Matasa. A karkashin cibiyar ne Hawwa ta bullo da wadanda dabaru da za su taimaka wajen rage yawan mutuwar jarirai da masu haihuwa a Jihar Taraba. Daga baya kuma ta shigar da wani tsari na kiwon lafiya da nufin ilmantar da mata wajen kiyaye harbin uwa ga danta dangane da ciwon kanjamau.
Wannan yunkuri da Hawwa ta yi, ya shero matar shugaban kasa, Hajiya Turai ’Yar’aduwa har ta ja ta a jika, lamarin da ya sa take shigar da ita cikin kusan kowace irin harka da za a gudanar a nan cikin gida Najeriya ko a kasashen waje.  A halin da ake ciki kuma an nuna sun shaku da Uwargida Dame Patience Johnathan.
Bayan Hadari
Muqaddashin gwamna Garba Umar na Jihar Taraba      Misis Hawwa Suntai ta yi namijin kokarin tsayawa kusa da mijinta a tsawon lokacin da yake jinya a asibitin Jamus don yin duk abin da ake bukata da zai taimaka wajen samun sauki ko ma waraka gaba daya.  A cikin irin wannan karakaina ne ta haifi ’yan biyunta.  Sannan daga baya, abin da ya auku, ya auku aka mayar da shi wata asibiti a Amurka.   
Bayan watanni 10, Hawwa na gefen mijinta, sai kwaram aka maido shi gida Najeriya daga asibitin John Hopkins da ke Amurka din da zimmar ya samu sauki kuma yana iya ci gaba da gudanar da mulkin jihar ta Taraba.  Wannan lamari ya haifar da kace-nace mai yawa da zafi, ganin yadda gwamnan ko iya fitowa bai yi daga jirgin da aka kawo shi ba, sannan ko magana ma sai dakyar-dakyar yake yi.
Duk wannan lamari ya gudana ne kuwa tare goya bayan wadansu jiga-jigan siyasar jihar, musamman Sanata Emmanuel Bwacha da yake wakiltar Kudancin Taraba, wanda kuma aka nuna shi ne zai gaji Gwamna Suntai a shekarar 2015 da kuma wani hamshakin lauya, Damian Dodo (SAN) da yake Abuja, wanda kuma ake fadin irin shunin da yake damawa.  Baya ga su, akwai da yawa daga cikin kwamishinonin jihar da kuma wadansu da ke wajen gwamnati.
Fitattu da suka rika suka mai ma’ana kan Uwargida Hawwa a jihar sun hada da tsohon shugaban majalisar jihar ta Taraba, Habu Isa Ajiya da tsohon shugaban jam’iyyar ACN, danjuma Munga, wandanda suka bayyana ya kamata a bar gwamnan ya murmure sosai kafin a yi ta tunanin komawarsa kan kujerarsa.  
Wasu da ke kusa da uwargidan kamar Abdulrazak Umar, kodineta na kungiyar Ceto Jihar Taraba, ya yi duk abin da yake iyawa ga ganin ya bayyana matsayin matar gwamna na mai tausayi da kula da sha’anin mijin nata, amma an jefa ta cikin sarkakkiyar siyasar jihar.
Mista Joel Ikenya, wanda tsohon sanata ne da ya wakilci Kudancin Taraba a jam’iyyar PDP, amma yanzu yana daga cikin jiga-jigan APC kuma yake hango kujerar gwamna a shekarar 2015, yayin da yake tsokaci kan matsayin Hawwa game da siyasar Taraba, ya ce ana iya zarginta idan tana goyon bayan maigidanta kan komawar mulki Kudancin Taraba.  Wannan dalili kuwa shi zai sa Sanata Bwacha ya tsaya mata, amma idan yana yin hakan ne saboda yana hango kujerar gwamna din shi ma, to wata magana ce ta daban da ke nuna yana goyon bayan ne saboda samun biyan bukatar kansa.
kokarin Daidaita Al’amura
A yunkurin daidaituwar al’amurra, jam’iyyar PDP ta nada wata tawaga ta binciko hakikanin matsayin lafiyar Gwamna Suntai, a karkashin jagorancin Sanata Hope Uzodinma, ina Uwargida Hawwa ta bude musu gaskiya lamari, abin da ya sa aka sami wata matsaya cewa shi mataimakin gwamna Garba Umar ya ci gaba da rike ragamar mulki kafin wattsakewar Gwamna Suntai.
Tun farko kuwa sai da Hawwa ta barke da kuka a gaban ’yan majalisar dokoki na jihar ta Taraba, a yayin da suka je don saduwa da Gwamna Suntai, suka ga halin da yake ciki, bayan da aka soma yada jita-jitar suna shirin tsige shi.  A yayin ziyarar ne Uwargida Hawwa ta amince da’yan majalisar a kan wadansu al’amurra da dama, ciki har da barin mataimakin gwamnan ya ci gaba da rike ragamar mulki.
Wani lamarin da yake nuna cewa an yi amfani da Uwargida Hawwa ne a cikin wannan tirka-tirka duka shi ne a yayin da tsohuwar ministar albarkatun ruwa, Misisi Solome Jankada ta bayyana tattaunawar da aka yi a boye tsakanin tawagar PDP da Gwamna Suntai a Jalingo.  Ta ce baya ga Sanata Bwacha, wanda suke daga yanki daya, “Kowa ya yarda da batun cewa an goyi bayan abin da shugaban majalisar dokokin jihar ya fada na cewa, ‘Muna son gwamnanmu a matsayinsa na Gwamnan Jihar Taraba har yanzu, amma mun fi son shi fiye da kasancewarsa a kan kujerarsa, saboda haka muna son ya je ya natsa don ya samu lafiya, ya wattsake’ ”.
A halin da ake ciki dai lamarin makomar siyasar Jihar Taraba ya yi harshen damo.  Ga dai batun komar da mulki Kudancin Taraba a 2015, inda ake jin cewa na kusa da gwamna wato Sanata Bwaca shi ne mai jiran gado. Ga kuma ’yan a bi sarki a sha kida da lagwada, wadanda ba su da tagomashi a gwamnatin Suntai, amma sun sami karbuwa a sabon canji, saboda haka ba za su so a koma ’yar gidan jiya ba.
Ko me ke akwai dai, lokaci mai canja al’amura, muna nan muna ji muna kuma saurare!  Ita kuwa Uwargida Hawwa, tunda an ce mukaddashin gwamna ya rika tuntubar maigidanta a kan wadansu manyan al’amura, ma ga irin salon rawar da za ta ci gaba da takawa!