✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hayakin janareta ya kashe wani direba da bakanike

Wani direban bas mai suna Kunle da bakanike fanalbita mai suna Sule sun mutu sakamakon shakar hayakin janareta a garejin da ke kan titin Bola…

Wani direban bas mai suna Kunle da bakanike fanalbita mai suna Sule sun mutu sakamakon shakar hayakin janareta a garejin da ke kan titin Bola a unguwar Ebute-Metta da ke Legas.
Wani abokin aikinsu mai suna Samsom ya ce lamarin ya auku lokacin da Kunle da Sule suka kulle kansu tare da janaretan da suka kunna a cikin garejin sakamakon ruwan sama. “Kunle ya kawo wa Sule aiki bai kammala ba har dare ya yi, sai suka yanke shawarar kwana a gareji domin kammala aikin. Suna cikin aiki, sai aka dauke wuta sakamakon ruwan sama, Sule ya kunna janareto, suka shigar da shi cikin garejin kuma da ma kofar a kulle take, babu inda iska take shiga. Bayan sun kammala aiki, sai barci ya kwashe su. Wanshekare da na zo, sai ga gareji a kulle kuma ga janareto yana aiki, ina budewa sai na gansu a kwance da na taba su, sai na ga kamar sun mutu, sai na kira jama’a muka kai su asibiti, inda aka tabatar mana sun mutu”. Inji shi.
Ofishin ’yan sanda da ke yankin ya tabbatar da faruwar lamarin, amma a hedikwatarsu jami’ar hulda da jama’a ta ce ba ta sami labarin aukuwar lamarin ba.