✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Herrera ya ja kunnen Manchester United da su ci gaba kwazo

Dan wasan tsakiya na Manchester United kuma daya daga cikin manyan ’yan wasan kungiyar Ander Herrera ya gargadi ’yan wasan kulob din da kada su…

Dan wasan tsakiya na Manchester United kuma daya daga cikin manyan ’yan wasan kungiyar Ander Herrera ya gargadi ’yan wasan kulob din da kada su gaza wajen sa kwazo musammam a watan nan da za su buga manyan wasanni.

Herrera  wanda dan asalin kasar Spain ne ya bukaci ’yan wasan su kara sa kaimi bayan  nasarar da suka samu wajen doke Leicester City da ci daya da nema a filin wasa na King Power wato gidan Leicester City duk da cewa yanzu haka suna samun nasarori.

Kocin rikon kwarya, Ole Gunnar Solskjaer ya ci wasa tara da kunnen doki daya a jere tun bayan da ya maye gurbin Jose Mourinho wanda United ta sallama a watan Disamba.

Hakan ne ya kai United mataki na biyar a teburin Firimiya ta Ingila, kuma maki biyu ya rage tsakaninta da Chelsea wadda take ta hudu.

United za ta ziyarci Fulham a gasar ta Firimiya gobe Asabar, sannan za ta karbi bakuncin kungiyar Paris St Germain wato PSG a gasar cin Kofin Zakarun Turai a ranar 12 ga watan Fabrairu kamar yadda BBC ya ruwaito.

Daga nan ne United za ta buga gasar Kofin FA zagaye na biyar, inda za ta ziyarci Chelsea ranar 18 ga watan Fabrairu, sannan ta karbi bakuncin Liberpool a gasar Firimiya.

Don haka ne Herrera ya bukaci ’yan wasa su mai da hankali wajen karawa da Fulham, kafin su hangi sauran wasannin da za su fafata masu zafi a cikin watan nan.