✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hidindimun Gizagawa

A wannan mako, za mu fara ne da jajantawa. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah Ya yi wa Malam Sambo rasuwa. Marigayin, shi ne…

A wannan mako, za mu fara ne da jajantawa. Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un! Allah Ya yi wa Malam Sambo rasuwa. Marigayin, shi ne mahaifin Barista Nuhu Sambo, Lauyan Kungiyar Gizago (08066366043). A madadin shugabanni da mambobin Kungiyar Gizago, muna mika ta’aziyyarmu ga dukkan ’yan uwa da iyalai. Allah Ya jikansa da rahma, amin.

***

A labarin farin ciki kuwa, Kungiyar Gizago na gayyatar dukkan ’yan uwa da abokan arziki zuwa wajen daurin auren tsohon Mataimakin Shugaban Kungiyar Gizago ta Najeriya, Malam Ibrahim Hamisu (08060651676). Za a daura auren nasa ne a jibi Lahadi da misalin karfe 11:00 na safe, a Unguwar Fagge, Layin Sama’ila Maiguza, Makarantar Malam Sani, Kano. Allah Ya sanya albarka, Ya ba da hakurin zama da juna, amin.