✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

HIKIMA

Barkan mu da sake saduwa a cikin wannan makon in da zamu yi karatu daga cikin littafi mai tsarki a kan hikima da kuma gargadi…

Barkan mu da sake saduwa a cikin wannan makon in da zamu yi karatu daga cikin littafi mai tsarki a kan hikima da kuma gargadi a gare mu mutane don mu yi tafiya cikin tafarkin Ubangiji ta wurin amfani da hikiman da ya bamu.

Karatun mu yana cikin littafin Karin Magana.

Dana, ka kasa kunne ga koyarwar mahaifinka, ka mai da hankali ga abin da mahaifiyarka take fada. Koyarwarsu za ta inganta halinka, ta zama kayan ado kamar kyakkyawan rawani a kanka, ko kyakkyawan abin wuya a wuyanka, don su kara maka kyau.

Dana sa’ad da masu zunubi suka jarabce ka, kada ka yarda in suka ce maka, “Zo mu tafi mu nemi wani mutum mu kashe, mu je, mu fāda wa marasa laifi mu ji dadi! Ba mu damu da ransu da lafiyarsu ba, mu dai mu tafi mu kashe su, mu hallaka su dungum. Za mu sami dukiya iri iri, mu cika gidajenmu da ganima! Ka zo ka hada kai da mu, dukanmu kuwa za mu raba abin da muka sato.”

Dana, kada ka gama kanka da irin wadannan mutane, ka yi nesa da su. Ba su kasalar aikata mugunta, kullum a shirye suke su yi kisankai. Ba shi da amfani a kafa tarko a idon tsuntsun da ake so a kama. Amma wadannan irin mutane kansu suke kafa wa tarko. Ba za su kama kome ba, sai rayukansu. Yin fashi yakan zama sanadin mutuwar ɗan fashi a koyaushe. Wannan shi ne abin da yakan sami kowane mutum da ya kama sana’ar sata.

Dana kada ka manta da abin da na koya maka. Kullum ka tuna da abin da na fada maka ka yi. Koyarwata za ta ba ka tsawon rai da wadata. Kada ka yarda ka rabu da biyayya da aminci, ka daura su a wuyanka, ka rubuta su kuma a zuciyarka. Idan ka yi wannan kuwa, Allah zai yi murna da kai. Za ka yi nasara cikin huldar da kake yi da mutane.

Ka dogara ga Ubangiji da zuciya daya, kada ka dogara ga abin da kake tsammani ka sani. A cikin dukan abin da kake yi, ka tuna da Ubangiji, shi kuma zai nuna maka hanyar da yake daidai. Sam, kada ka yarda ka dauki kanka kai mai hikima ne fiye da yadda kake, kai dai ka ji tsoron Ubangiji, ka rabu da aikata mugunta. Idan ka kiyaye wannan, zai zama maka kamar magani mai kyau, ya warkar da raunukanka, ya kuma sawwake maka azabar da kake sha. Ka girmama Ubangiji ta wurin mika masa hadaya daga mafi kyau na amfanin gonarka. Idan ka yi haka rumbunanka za su cika da hatsi. Za ka sami ruwan inabi mai yawa, har ka rasa wurin da za ka zuba shi duka.

Dana, sa’ad da Ubangiji ya tsauta maka ka mai da hankali sosai, ka kuma yarda da gargadinsa. Ubangiji yana tsauta wa wadanda yake kauna. Kamar yadda mahaifi yakan tsauta wa dan da yake fāriya da shi. Mai farin ciki ne mutumin da ya zama mai hikima, ya kuma sami fahimi. Yana da riba mai yawan gaske fiye da ta azurfa, tamaninta a gare ka ya fi na zinariya. Tamanin hikima ya fi na lu’ulu’ai, ya kuma fi kowane irin abin da kake so tamani. Hikima takan tsawanta ranka, ta kuma ba ka dukiya da daraja. Hikima takan sa ka ji dadin zama, ta kuma bi da kai lafiya a zamanka. Masu farin ciki ne wadanda suka sami hikima, hikima za ta ba su rai kamar yadda itace yakan ba da ‘ya’ya.

Ubangiji ya halicci duniya ta wurin hikimarsa, Ya shimfida sararin sama a inda yake ta wurin saninsa.

Hikimarsa ta sa ruwan koguna ya yi gudu, Gizagizai kuwa su zubo da ruwa bisa duniya.

dana ka rike hikimarka da basirarka. Ko kusa kada ka bari su rabu da kai. Za su tanada maka rai, rai mai dadi da farin ciki. Za ka bi hanyarka lafiya lau, ba ko tuntube. Ba za ka ji tsoro, sa’ad da kake kwance a gadonka ba, za ka yi ta sharar barci a dukan dare. Ba za ka damu da masifar da za ta auko farat daya ba, irin wadda takan auka wa mugaye kamar hadiri. Ubangiji zai kiyaye ka. Ba zai bari ka fāda cikin tarko ba.

Dana, ka koyi abin da nake koya maka, sam kada ka manta da abin da na fada maka ka yi. Ka kasa kunne ga abin da yake na hikima, ka yi kokari ka fahimce shi. I, ka roki ilimi da tsinkaya. Ka nema da iyakar kokarinka kamar yadda za ka nemi azurfa, ko kowace irin boyayyiyar dukiya. Idan ka yi za ka san abin da ake nufi da tsoron Ubangiji. Za ka yi nasara a kan koyon sanin Allah. Ubangiji ne yake ba da hikima. Ilimi da fahimi kuwa suna cikin kalmominsa. Shi yake tanada wa adalai taimako da kiyayewa, wato mutane masu aminci. Yakan kiyaye wadanda suke lura da kyau, ya kiyaye waɗanda suke dogara gare shi.

Idan ka kasa kunne gare ni za ka san abin da yake daidai, da abin da yake gaskiya, da abin da yake na kirki. Za ka san abin da za ka yi. Za ka zama mai hikima, iliminka zai faranta maka rai. Tsinkayarka da fahiminka za su tsare ka. Za su hana ka aikata mugayen ayyuka, za su nisantar da kai daga mutane masu ta da hargitsi da irin maganganunsu, mutane wadanda suka bar zaman adalci don su zauna cikin duhun zunubi, wadanda suke jin daɗin yin laifi, suna nishaɗi cikin mugunta. Ba za a dogara da su ba, ba kuwa za a iya amincewa da su ba.

Bari Ubangiji Allah ya taimake mu wajen yin amfani da hikiman da Ya bamu.