Da Dumi Dumi

Hira da Sashin Hausa na BBC kan Bikin Ranar Tsabtace Intanet ta Duniya (1)

Sabanin yadda muka saba kwararo bayanai kan maudu’in da muke magana a kai na tasirin ci gaban kimiyya da fasahar sadarwa kan rayuwa da dabi’u da jinsin dan Adam a duniya, a yau ina tafe ne da wani guzuri da na yi mana daga zauren gabatar da shirye-shirye na sashin Hausa na BBC da ke nan Abuja.  Wannan hira ce da aka yi da ni don fito da muhimmancin Ranar Tsabtace Fasahar Intanet (World Safer-Internet Day) ta bana, wadda ake gudanarwa a duk ranar 11 ga Fabrairun kowace shekara.  Manufar samar da wannan rana dai ita ce don wayar da kan jama’a kan hadura da matsalolin da ke tattare da fasahar Intanet, tare da samar da hanyoyin kariya musamman ga kananan yara da matasa.

Sashen Hausa na BBC da ke nan Abuja, kamar yadda ya saba, ya gayyace ni don hira ta musamman kan muhimmancin wannan rana da kuma shawarwari ga iyaye da matasa da dukkan masu ruwa-da- tsaki wajen mu’amala da Intanet.  An sanya wannan hira ce a shirin rana (na karfe 3 na yamma) na ranar Litinin, 10 ga Fabrairu.  Kasancewar ba dukkan hirar ake sanyawa ba saboda karancin lokaci, na ga dacewar rubuce hirar baki dayanta, don bai wa masu karatu musamman wadanda ba su saurari shirin ba, damar amfana da abubuwan da hirar ta kunsa.  A sha karatu lafiya.

BBC: To, da farko za mu so mu ji me wannan rana ta kunsa da kuma muhimmancinta?

Baban Sadik: Wannan rana ta “World Safer-Internet Day” dai, kamar yadda aka ji sunan ko taken a Ingilishi, rana ce da ake kokarin wayar da kan jama’a don samar da muhallin Intanet tsabtatacce a ilahirin duniyar Intanet baki daya, ta yadda zai zama duk wanda ke mu’amala ko tu’ammali da wannan fasaha ya yi mu’amala da ita ba tare da wata cutarwa ba; yana mai samun bayanan da yake bukata, ta hanyoyin da yake bukata.  Muhimmancin wannan rana dai zai bayyana mana ne idan muka yi la’akari da cewa samun muhalli mai dauke da lumana a Intanet shi ne zai taimaka wa duk wani mai gudanar da kasuwanci ko binciken ilimi ko karatu ta hanyar da zai samu damar yin haka ba tare da fuskantar wata cutarwa ba ko wata fargaba.

 

ADVERTISEMENT

BBC:  Kamar wasu matakai ka ke ganin iyaye ko ’yan uwa za su rika bibiyar shafukan da ’ya’yansu ko kuma wadanda suke karkashinsu suke ziyarta musamman ta la’akari da shafukan da ba su kamata ba a wannan zamani?

Baban Sadik:  Wato iyaye ko ’yan uwa su bibiyi ’ya’yansu ko ’yan uwansu misali, don tabbatar da cewa ba su afka cikin matsala a wannan muhalli ba, abu ne mai wahala matuka, a tare da cewa abu ne mai yiwuwa. Idan muka lura a yau galibin kayayyaki da hanyoyin sadarwa na zamani da wayoyin salula suna zuwa ne da wani bangare da ake kira: Parental Control. Wannan bangare na Parental Control an samar da shi ne a na’urorin sadarwa don bai wa iyaye damar aiwatar da wani aiki da malaman fasahar sadarwa da aikin jarida ke kira da sunan: Gate keeping. Shi tsarin Gate keeping shi ne, ya zamanto a matsayinka na uba, ko uwa, ko malami, ko kuma mai tarbiyya, ka iya tantance hanyoyin da wanda ka ke tarbiyya ko lura da shi zai iya cutuwa daga gare su da tanadar hanyoyin kariya gare shi ba tare da hakan ya hana shi mallakar abin da yake bukata ko kasancewa a wani muhalli ba, muddin lalura ta kama ya kasance a muhallin ko ya mallaki abin.

Wannan tsari na Gate keeping yana da muhimmanci matuka, kuma aiwatar da shi abu ne mai sauki a galibin kasashe da suka ci gaba. Domin kwamfutocin sun yawaita, kuma ‘ya’yansu na amfani da su ne galibi ko dai a gidajen wasan kwamfuta (Computer Game Centers) ko kuma a gidajensu.  Idan ma ta hanyar wayoyin salula ne, suna da hanyoyi da dama da suke iya bibiyarsu don tabbatar da abin da suke ciki.  Amma a nan, wato a kasashe masu tasowa, musamman muhalli kamar Najeriya ko Arewacin Najeriya, za ka samu da yawa cikin yara da matasa suna amfani da wayoyin salula ne musamman wajen mu’amala da fasahar Intanet. Kuma kokarin tantance wani shafi ko shafuka yaro ke shiga, yana bukatar sai ka dauki wayar ka rike, ka dudduba lokaci-lokaci, musamman. Idan kuma yana goge shafukan da yake shiga, ka ga akwai matsala (gane hakan zai yi wahala).

Don haka, hanya mafi sauki ita ce, iyaye su yi kokarin ilimantar da ’ya’yansu kan munanan hanyoyin da wannan fasaha ta Intanet ta kunsa. Akwai abubuwa da dama da suke miyagu ne; kamar dai rayuwar da muka saba yi ne a zahiri. Idan ba ka da ilimi kan (munin) abu, za ka iya fadawa cikin matsala. Don haka abu na farko dai shi ne fadakar da su cewa akwai abubuwa masu hadari a wannan muhalli. In so samu ne ma suna iya bayyana musu hakikanin wadannan wurare (idan sun sansu ke nan), su rika musu lacca sosai lokaci-lokaci.

Za mu ci gaba a mako mai zuwa.

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya