✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hira da Sashin Hausa na BBC kan Bikin Ranar Tsabtace Intanet ta Duniya (3)

Kamar yadda muka fara kawo wa a makonni biyu da suka wuce, yau ma za mu ci gaba da hirar da Sashin Hausa na BBC…

Kamar yadda muka fara kawo wa a makonni biyu da suka wuce, yau ma za mu ci gaba da hirar da Sashin Hausa na BBC ya yi dani don bikin Ranar Tsabtace Intanet a Duniya na shekarar 2020, wanda ya gudana a ranar Talata, 11 ga Fabrairu.  A yau mun dauko ragowar hirar ce.  A sha karatu lafiya:

BBC Hausa:  Za ka iya gaya mana wasu matakai ne masu amfani da Intanet za su dauka domin kare kansu daga wadannan shafuffuka (munana) da wasu shafuffukan da ba su kamata ba?  Musamman ganin cewa wasu lokutan kana cikin amfani da Intanet sai a rika yi maka tallar irin wadannan shafuffuka?

Baban Sadik: Abu na farko dai shi ne, mai mu’amala da fasahar Intanet ya zama yana da manufa.  Mece ce manufarsa ta amfani da fashar Intanet – a wayar salula ce ko a kwamfuta ce?  Idan manufarsa bincike ne na ilimi, ko karatu don karuwar fahimta, ko kasuwanci yake yi ko kuma kawai don sadarwa ce. Abu mai muhimmanci dai shi ne ya zama yana da manufa. Kada ya zama don ya ga wadansu na amfani da fasahar ce kawai shi ma ya ce bari ya yi. Idan haka ta kasance, to, zai yi ta walagigi ne kawai.

Abu na biyu shi ne, bayan kasancewarsa yana da manufa, ya zama ya tabbata a kan wannan manufa tasa a koyaushe. Duk wani abin da ba ya cikin manufofinsa, to ya yi kokari ya kawar da kansa daga gare shi. In har ma zai yi mu’amala da wani abin da ba ya cikin manufarsa, to, ya zama wannan abu yana daga cikin abubuwan da za su taimaka masa ne wajen cimma waccan manufa tasa, ko kuma fadada fahimtarsa kan manufar da yake son cimmawa. A takaice dai, ya zama duk wani abin da ba ya da alaka da manufarsa, kada ya ba shi wani muhimmanci.

Abu na uku shi ne, ya yi kokarin wayar da kansa kan wannan fasaha ta Intanet. Ya tambayi kansa mece ce Intanet? Kuma daga ina wadannan shafuffuka da yake mu’amala da su suke samuwa? Sannan ya rika tambayar kansa a kullum, shin duk abin da nake gani ko nake mu’amala da shi a Intanet din nan daidai ne, ko akwai wasu abubuwan da ake sanya su da wata manufa (da ta sha bamban da samar da fa’ida)? Domin bayanan da muke mu’amala da su a Intanet sun kasu kashi uku ne: na farko akwai abin da yake tsantsar amfani ne; an zuba shi ne don samar da fa’ida ga mai ziyara ko mu’amala da shi. Na biyu kuma su ne nau’o’in bayanan da suke dauke da amfani da kuma cutarwa. Wadannan su ne galibin bayanan da suka shafi tallace-tallace misali, musamman a kafafen sada zumunta. Sannan na uku su ne nau’o’in bayanan da suke tsantsar cutarwa ce, babu wata fa’ida da suke bayarwa. Su kuma wadannan ba a ganinsu a ko’ina, sai in ka je inda suke. Wannan shi ne hakikanin gaskiya. Musamman shafuffukan batsa; da wahala kana hawa Intanet kawai ka ga shafuffukan batsa.

Eh, na yarda za ka iya cin karo da hotunan mata da dan tofi haka, ko ka ga mace gashin kanta a bude haka (ko wani bangaren kirjinta a bayyane). Wannan ya faru ne saboda masu galibin wadannan shafuffuka ba su yarda cewa mace ta rufe gashinta yana da wata alaka da ci gaban rayuwa ko addini ba. Ka ga wannan daban.  Su a gare su wannan shiga ce ta al’ada.  Amma ka ga mace tsirara haka kawai a Intanet (da wahala), sai in ka kutsa inda ke dauke da wadannan ire-iren bayanai. Haka ma duk wani abin da ya shafi hotunan bidiyo, in dai na batsa ne, to, za ka samu sai in mutum shi ya kai kansa wannan wuri. Don haka dai a takaice, duk abubuwan da suke da alaka da harkoki na cutarwa irin su batsa da irin wuraren da ake zambatar mutane da sauransu. To, za ka samu sai in mutum ne da kansa ya yi mu’amala da masu ire-iren wadannan shafuffuka.

Abu na hudu shi ne, idan abota kake yi da mutane a shafuffuka ko ta manhajojin sadarwa irin su Whatsapp da Facebook da sauransu, to, na farko dai tukun mu sani, Dandalin Facebook matattara ce wacce take babbar matattara (a Intanet).  Daya daga cikin masana harkar sadarwa da kariyar bayanai (Information Security) mai suna: Graham Cluly – babban jami’i a kamfanin Sophos – yana cewa a duniyar Intanet gaba daya babu wurin da ya fi hadari irin Dandalin Facebook. Babu wurin da ake da tarin mazambata da ’yan dagaji da ’yan ta’adda da ’yan kashe-mu-raba irin Dandalin Facebook. A takaice dai, Dandalin Facebook matattara ce da ke dauke da duk wani bala’i da ka sani a duniyar Intanet.  To, amma kai idan ka shiga wajen, me ke baka kariya ko rashin kariya? Su ne irin abokan da kake mu’amala da su. Idan mutanen kirki ne, shi ke nan. Amma idan ka sake ka kutsa kanka wancan wuri inda ’yan rudu suke, to, duk wadancan abubuwa da Graham Cluly ya siffata, su ne za su shafi mutum. Don haka, wannan ke nan. Ka san inda za ka je, sannan da irin mutanen da za ka yi mu’amala da su; idan wuri ne da ake tattaunawa misali.

Sannan (abu na biyar), idan kana mu’amala da mutane a wadannan kafafe na sadarwa irin su Whatsapp ko Facebook ko zaurukan Imel – irinsu “Yahoo Groups” ko “Google Groups” – misali, yana da kyau ka san cewa, ba dukkan adireshin Intanet (Internet link) da aka aiko ba ne za ka latsa don ganin me ke ciki. Haka ba dukkan bayanan da aka aiko ko tunkudo zauren ba ne yake daidai. Akwai sakonni da yawa wadanda suke na bogi ne, wato: “Fake News.”  Kai, a takaice ma dai, kusan kashi 70 ko 80 cikin 100 na sakonnin da ake musayarsu a wadannan kafafe, duk sakonnin bogi ne. Duk galibin sakonnin da ake tunkudo su (Forwarded message), da yawa za ka samu wani kato ne ya zauna ya kirkiri wani labari don samar da wani yanayi da yake son ya shigar cikin kwakwalen masu karantawa da sunan fadakarwa, ko wata harkalla ce ta kasuwanci da aka kawo da sunan “garabasa,” ko wata karya da aka yi wa Allah da ManzonSa aka lullube ta da sunan “falala” – ma’ana dai, karairayi ne zalla ake shiryawa. Abu ne sananne dama cewa labarun karya (Fake News) da sakonnin bogi (Spam messages) abubuwa ne guda biyu da suka fi komai addabar jama’a a duniyar Intanet, kuma ana amfani da wadannan kafafe ne wajen yada su cikin sauki.

Abu na karshe shi ne, mutum ya gaya wa kansa gaskiya. Idan kana gaya wa kanka gaskiya wajen mu’amala da wadannan kafafen sadarwa, to ba za ka samu matsala ba. Amma idan mutum bai gaya wa kansa gaskiya, kawai yana bin duk abin da ya ga ya burge shi ne kawai, to, zai fada cikin bala’i.  Allah sawwake.