✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hira da Sashin Hausa na BBC kan Bikin Ranar Tsabtace Intanet ta Duniya (4)

Kamar yadda muka fara kawowa a mako uku da suka wuce, yau ma za mu ci gaba da hirar da Sashin BBC Hausa ya yi…

Kamar yadda muka fara kawowa a mako uku da suka wuce, yau ma za mu ci gaba da hirar da Sashin BBC Hausa ya yi da ni don bikin Ranar Tsabtace Intanet a Duniya na shekarar 2020, wanda ya gabata a ranar Talata, 11 ga Fabrairu. Wannan kashin karshe ke nan na hirar.  A sha karatu lafiya.

BBC Hausa:  Tambaya ta karshe ita ce, taken shirin na bana shi ne: “Hada Hannu Don Samar da Tsabtatacciyar Fasahar Intanet a Duniya.”  Wace irin gudunmawa kake ganin kowa zai iya bayarwa don tabbatar da hakan?

Baban Sadik:  Masu ruwa-da-tsaki cikin lamarin fasahar Intanet a duniya sun hada da iyaye da ’ya’yansu da ’yan uwa da hukumomin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kansu, da wadanda suke da alhakin zuba bayanai a kafafen da ke wannan fasaha mai matukar tasiri.  Wadannan su ake kira: “Stakeholders” a harshen Ingilishi.  Ma’ana wadanda suke da ruwa-da-tsaki wajen gudanuwa da kuma aiwatar da mu’amala ko harkoki a wannan muhalli na Intanet a duniyar yau.

Su iyaye dole ne su lura da ’ya’yansu, su kuma ba su tarbiyya, wanda shi ne abin da yake da muhimmanci na farko. Sannan idan suka fara amfani da wadannan na’urori da kafafen sadarwa na zamani, zama bai gansu ba – kada su ce ai mun riga mun ba  su tarbiyya shi ke nan.  Dole su rika lura da su.  Idan suka fahimci abin da suke gudanarwa mai amfani ne, to, sai su ci gaba da ba su shawarwari kan hanyoyin da za su taimaka musu wajen samun karin fa’ida da amfani.

Su kuma matasa da ke mu’amala da wadannan kafafe na sadarwa kuma su ji tsoron Allah; su rika gaya wa kansu gaskiya.  Duk abin da wani ya ja zuwa gare shi, wanda ya saba wa irin tarbiyyar da iyayensu suka ba su, to, su yi kokari su nisance shi. Su sani, wannan shi ne zaman lafiya gare su.  Duk mutumin da bai bi maganar iyayensa ba ya ci ga da kutse-kutse, to, wata rana zai kutsa wani wurin da idan ya shiga, ba zai iya fitowa ba. Akwai abin da ake kira da suna: “Internet Blackhole.” Wannan kalma ta “Internet Blackhole” tana ishara ce ga wani wuri mafi muni da ke giza-gizan sadarwa ta Intanet. Ba wai wani wuri ba ne takamaimai, balle ka ce idan ka san wurin shi ke nan za ka guje masa. Wuri ne da ya fi ko wane wuri hadari a Intanet. Muddin mutum ya sake ya fadawa cikinsa, kuma ya yi mummunar sabo da wannan wuri, to, ba zai taba iya fitowa daga ciki ba har tsufa ko karshen rayuwarsa. Kamar yadda idan mutum ya fada rijiya mai gaba dubu, ba zai iya fitowa daga cikinta ba.  Ire-iren wadannan wurare dai sun hada da shafuka ko gidajen yanar sadarwa na batsa da shafukan caca da wuraren da ake ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma shafukan da ake koyon duk wani nau’i na zamba-cikin-aminci (“Internet scam” ko “419”) a Intanet. Wurare ne da suka fi kowane wuri hadari a Intanet.

A bangaren hukuma kuma dole ne a ci gaba da wayar da kan jama’a, kamar yadda na zayyana a baya. Hukuma ta san cewa al’umma fa amana ce a hannunta.  Sannan idan jama’a kansu ya waye kan wannan fasaha, za su san mene ne mummuna da abubuwan da suke masu amfani a wannan muhalli. Idan haka ya samu kuwa, in Allah Ya so, yawan laifuffukan da ake aikatawa ta hanyar Intanet, irin su zamba-cikin-aminci musamman, za su ragu cikin al’umma.  Wanda daman wannan matsala na cikin abin da ke ci wa gwamnatin Najeriya tuwo a kwarya, kamar yadda tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki ya taba bayyanawa lokacin da aka gayyace shi wani taro kan samar da hanyoyin tsaron kasa a kafafen sadarwa na zamani, shekara kusan hudu da suka gabata.  Ya ce Najeriya na hasarar biliyoyin Naira sanadiyyar masu zamba-cikin-aminci ta hanyar Intanet a Najeriya a duk shekara.  Idan hukuma ta ci gaba da wayar da kan jama’a in Allah Ya so wannan zai ragu.

Sannan har wa yau, galibin kamfanonin da ke kera na’urorin sadarwa, musamman kwamfuta da wayoyin salula, kan sanya wani bangare da suke kira: “Parental Control,” wato tsarin da ke bai wa iyaye damar toshe duk wata kafa da za ta iya jefa rayuwar kananan yara cikin hadari a na’urorin sadarwa. Idan iyaye suka tsara na’urorin sadarwar da suka saya wa ’ya’yansu gabanin su mika musu, hakan zai taimaka musu. Su ma yara za su iya taimaka wa kansu ta amfani da wannan tsari ko wasu tsare-tsare da ke sauka kan wayar salula da kwamfuta, musamman bangaren da ke lura da kalmomin hani a yayin mu’amala da manhajar nemo bayanai a Intanet. Suna iya bai wa wayar ko kwamfutar umarnin cewa duk sa’ar da wani ko su da kansu suka shigar da wata kalma mai suna kaza, misali, kada a budo musu. Duk da na san wannan ba abu ba ne mai sauki.

Idan aka bi wadannan hanyoyi da ma wasu da ban ambata ba, in Allah Ya so, za a samu sauki kuma a tsira daga matsala a wadannan kafafe na sadarwa. Allah  Ya yi mana jagora, amin.