Search
Subscribe
Hisba ta kama mai yanka awakin mutane a Jigawa

Hisba ta kama mai yanka awakin mutane a Jigawa

Hukumar Hisba ta Jihar Jigawa ta kama wani matashi da ake zargin ya kware wajen kama awakin mutane yana yankawa yana binne naman a kasa sannan ya gasa kayan cikin ya cinye.

Matashin mai suna Yunusa Idris, Hukumar Hisba ta ce ta kama shi ne a lokacin da ya kama tunkiyar wani Bafulatani da yake kiwon shanu a Unguwar Gida Dubu Yadin Dutse, inda ya kai ta wani kango ya boye da niyyar idan Bafulatanin ya wuce sai ya je ya yanka ta.

Bayan da Bafulatanin ya kada sauran shanunsa ya wuce ba tare da sanin an kama masa tunkiya ba ne, sai wanda ake zargin ya nufi kangon ba tare da sanin akwai wadansu daliban Jami’ar Tarayya da ke Jigawa (FUT) suna karatu a ciki ba.  A lokacin da ya isa kangon ne sai ya tambaye su labarin tunkiyar da ya boye a ciki, da suka fara yi masa tambayoyi ne sai ya nemi ya gudu inda nan take suka kama shi suka mika shi ga jami’an Hisba don ci gaba da gudanar da bincike.

Kwamandan Hisba na Jihar Jigawa Malam Ibrahim Dahiru ya ce da zarar hukumarsa ta kammala bincike za ta mika wanda ake zargin ga ’yan sanda.

Matashi Yunusa Idris ya ce ya dade yana satar awakin mutane.  Kuma ba ya cin naman, yana haka rami ne ya binne naman, yayin da yake gasa kayan cikin ya cinye.

Ya ce a baya an taba kai shi gidan yari  kan satar wata akuya bayan asirinsa ya tonu. Kuma da mahaifansa suka yi masa nasiha ne sai ya daina, amma daga baya ya koma ruwa saboda yana shan tabar wiwi.

Sai dai ya roki al’umma su yi masa addu’a don ya daina sata, inda ya ce ya san ba aba ce mai kyau ba. Kuma ya sha alwashin ba zai sake yin sata ba idan aka yafe masa a wannan karo.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin