✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta lalata kwalaben giya 196,400 a Kano

Jami’an Hukumar Shari’ah ta Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben giya sama da dubu 196,400 na giya da wasu kayan maye a cikin birnin…

Jami’an Hukumar Shari’ah ta Hisbah ta jihar Kano ta lalata kwalaben giya sama da dubu 196,400 na giya da wasu kayan maye a cikin birnin jihar. Sakataren watsa labarai na Mataimakin Gwamnan jihar Hassan Musa-Fage, ne ya sanar da hakan.

Hassan, ya sanar da hakan ne lokacin da hukumar ta yi aikin lalata kayan a garin Kalemawa da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa.

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya ce muslunci ya hana musulmi shan giya da sauran abin da zai sa shi maye wanda zai sa mutum jya fita hayyacinsa.

Gwamnan ya bukaci malami da su ci gaba da wayar da kan jama’a akan shan kayan maye.