✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hisbah ta lalata kwalaben giya miliyan biyu a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi bikin lalata kwalaben giya  da yawanta ya kai kwalba miliyan daya da dubu 960. Hukumar ta gudanar da…

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta yi bikin lalata kwalaben giya  da yawanta ya kai kwalba miliyan daya da dubu 960.

Hukumar ta gudanar da wannan aikin fasa kwalaben giyar ne a garin Hawan Kwalabe da ke Karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar bisa jagorancin Babban Kwamandan Hukumar  Sheikh Muhammad Sani Ibn Sina.

Da yake yi wa Aminiya karin haske game da aikin lalata giyar da hukumar ta gudanar  Mataimakin Kwamandan Hisbah Bangaren Ayyuka Malam Shehu Tasi’u Is’hak ya ce hukumar ta dauki tsawon wata shida tana tara giyar da ta yi nasarar kamawa a wurare daban-daban a fadin jihar da suka hada da  manyan titunan jihar  da kuma wasu mashaya. “Yawancin giyar da muka lalata mun kama ne a kan manyan titunan jihar a daidai lokacin da masu giyar ke kokarin shigowa da ita cikin jihar. Abin da muke yi shi ne muna datse giyar ce akan hanyar shigo da ita jihar wato ba mu bari ta kai ga shiga cikin gari ballantana a kai ga raba ta a wuraren sayarwa. Don haka yawancin giyar da muke kamawa muna kamata ce akan titunan shigowa jihar da suka hada da Titin Zariya da na Katsina da na Maiduguri. A wannan lokaci sai da muka samu kimanin mota 17. Giyar da muka samu a mashaya ba ta da yawa,” inji shi.

Mataimakin Kwamandan ya bayyana cewa, “Muna gudanar da wannan aiki ne ta hanyar bin hukuncin kotu. Kasancewar muna da dokarmu da ta ba mu damar kama kayan maye a fadin Jihar Kano don haka idan muka kama irin wadannan kaya muna kai wa kotu.  Ita kuma kotu za ta ci tarar masu kayan, sannan za mu nemi iznin kotun a kan ta ba mu damar lalata kayan, idan muka samu shalaewar kotu sai mu dauki kayan mu je a farfasa tare da konewa.”

Ya yi kira ga al’ummar jihar su ci gaba da ba Hukumar Hisbah hadin kai wajen tona asirin masu shigowa da giya ko masu aikata miyagun ayyuka ta hanyar sanar da hukumar duk inda suka san ana aikata ayyukan badala a fadin jihar.

“Mutane suna taimaka mana da bayanai don haka muke kara nemna hadin kansu bisa wanann aiki da muke yi, domin aiki ne na taimakon al’umma gaba daya.  Yanzu da a ce ba mu samu damar kama wannan giyar ba, to da tuni giyar tana cikin gari wanda kuma ’ya’yanmu ne za su shanye ta don haka muna godiya ga Allah bisa wannan aiki da muka gudanar,”  inji shi.