Da Dumi Dumi

Ya kuke kallon salon mulkin Buhari da gwamnoni?

Buhari ya kara cika shekara guda a kan mulki
Shugaba Muhammadu Buhari

Ranar 29 ga watan Mayu shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da wasu gwamnonin kasar ke cika shekara daya a zangon mulkinsu su na biyu kuma na karshe.

Shin kun gamsu da kamun ludayin gwamnatin Shugaba Buhari a shekarar farkon wa’adinsa na biyu?

Wane gwamna kuke ganin ya ciri tuta?

Daga cikin gwamnonin akwai wadanda a wannan ranar suke cika shekara daya a mulkinsu karo na farko.

Masu cika shekara daya su ne gwamnonin jihohin Legas da Ogun da Oyo a yankin Kudu maso yamma.

ADVERTISEMENT

Sai gwamnan jihar Zamfara daga Arewa maso yamma da kuma jihohin Borno, Yobe, Adamawa da Gombe a Arewa maso Gabas.

Cikonsu shi ne gwamnan jihar Nasarawa a Arewa ta tsakiya.

Ku fada mana ra’ayinku

Shin kun gamsu da salon mulkin Shugaba Buhari a shakarar farkon wa’adinsa na biyu?

Wane gwamna kuke ganin ya ciri tuta?

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya