✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotuna: Ranar yara ta duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar Laraba 27 ga watan Mayu a matsayin Ranar Yara ta Duniya, domin a hadu a tuna da mahimmacin yara…

Majalisar Dinkin Duniya ta ware ranar Laraba 27 ga watan Mayu a matsayin Ranar Yara ta Duniya, domin a hadu a tuna da mahimmacin yara tare da kare hakkokinsu.

Taken Ranar Yara ta bana shi ne yin tanadi ta hanyar inganta rayuwar yara, sai dai ba a samu damar yin bukukuwa kamar yadda aka saba ba saboda cutar coronavirus, wacce ta hana yin tarurruka a duniya.

Domin tunawa da yara (manyan gobe), mun kawo maku wasu tsaffin hotunan shugaban Najeriya Muhammadu Buhari tare da wasu yara da ya gana da su a lokuta daban daban.