✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotuna: Yadda dokar hana fita ta kasance a Plateau

Tun da karfe 12 na daren Alhamis ne dokar da gwamnatin jihar Filato ta kafa ta hana fita don kauce wa yaduwar cutar coronavirus ta fara…

Tun da karfe 12 na daren Alhamis ne dokar da gwamnatin jihar Filato ta kafa ta hana fita don kauce wa yaduwar cutar coronavirus ta fara aiki.

Wakilin Aminiya ya zagaya wasu sassan Jos, babban birnin jihar don ganin yadda dokar ke tafiya.

Ga dai abin da ya gane wa idonsa:

Gwamnan jihar Filato Simon Bako Lalong lokacin da yake kaddamar da shirin feshin maganin kashe kwayoyin cuta a jihar

 

Ma’aikata na feshin maganin kashe kwayoyin cuta a cikin garin Jos babban birnin jihar Filato

 

Wasu ma’aikatan na shirin fara feshin maganin kashe kwayoyin cuta a cikin garin Jos, babban birnin jihar Filato.

 

 Yadda wata unguwa a birnin Jos ta kasance fayau ranar juma’a bayan dokar hana fita ta fara aiki
Jami’an tsaro kawai ake iya gani a kan titi a wasu unguwannin Jos, babban birnin jihar filato

 

 

Nan wata unguwa ce inda duk shaguna ke a rufe.