✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hotuna: Yadda Shugaba Buhari ya yi sallar Juma’a

Al’ummar Musulmi a wasu sassan Najeriya sun gudanar da sallar Juma’a a karo na farko bayan da gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin…

Al’ummar Musulmi a wasu sassan Najeriya sun gudanar da sallar Juma’a a karo na farko bayan da gwamnatin tarayya ta sassauta wasu daga cikin dokokin da ta kafa da nufin hana yaduwar annobar COVID-19.

Sai dai kawo yanzu akwai jihohi da dama da ba su kai ga ba da umarnin bude wuraren ibada ba.

Amma a jihohin da aka ba da umarinin yin haka an samu sauye-sauye a wasu masallatan Juma’a, inda akasari aka sanya takunkumin rufe baki da hanci.

A wasu masallatan an ba da tazara; yayin da hakan ya kasa samuwa a masallatai da dama da wakilin Aminiya ya ziyarta.

Shi ma Shugaba Muhammadu Buhari ya yi tasa sallar ta Juma’a a Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja, ga kuma hotunan yadda ta kasance.