✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Kano ta haramta nuna “Kwana Casa’in”

Hukumar Tace Fina-Finai da Ayyukan Dab’i ta Jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma’il Afakalla ta ba gidan talabijin mai zaman kansa na Arewa 24 wa’adin…

Hukumar Tace Fina-Finai da Ayyukan Dab’i ta Jihar Kano, a karkashin shugabancin Isma’il Afakalla ta ba gidan talabijin mai zaman kansa na Arewa 24 wa’adin awa 48 da ya dakatar da haska fina-finan “Kwana Casa’in” da “Gidan Badamasi”, domin a cewarsa, fina-finan sun saba wa dokar Jihar Kano.

Kamar yadda wani sashi na takardar da hukumar ta aika wa hukumar gidan talabijin din, ta ce ta dauki matakin ne, musamman domin wasu sassa da aka nuna a fim din “Kwana Casa’in” sun saba da al’adun al’ummar Jihar Kano, musamman inda aka nuna wani mutum ya rungumi wata a cikin fim din a wani kantin sayar da kaya na Sahad Stores da ke Kano.

Hukumar ta ce tana da hakkin dubawa da tantance duk wani fim da aka shirya a jihar da Hausa, don haka suna bukatar kafin a ci gaba da haska fim din na “Kwana Casa’in”, sai ta tace shi tukunna.

Ko me hukumar gidan talabijin ta Arewa 24 za ta ce game da wannan umurni na Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano?

Aminiya ta tuntubi daya daga cikin marubutan fina-finan na “Kwana Casa’in” da “Gidan Badamasi”, Nazir Adam Salih, wanda ya shaida wa wakilinmu ta wayar tarho cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ba ta da hurumi dangane da al’amuran gidajen talabijin, don haka za su ci gaba da haska wadannan fina-finai kamar yadda suka saba.

Kamar yadda ya ce, a matsayinsu na Musulmi kuma Hausawa, suna iya kokarinsu wajen kare martabar addininsu kuma suna kauce wa duk wani abu da zai kawo matsala a wannan bangare.