✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Hukumar Cibil Defence ta kafa dakarun kare daji da gonaki a Bauchi

Hukumar Tsaro ta Cibil Defence (NSCDC), ta kafa dakarun kare dazuzzukan kiwo da gonaki masu suna Agro Rangers  a  Jihar Bauchi. A jawabinsa lokacin kaddamar…

Hukumar Tsaro ta Cibil Defence (NSCDC), ta kafa dakarun kare dazuzzukan kiwo da gonaki masu suna Agro Rangers  a  Jihar Bauchi.

A jawabinsa lokacin kaddamar da dakarun a Bauchi, Kwamandan Cibil Defense na Jihar Bauchi Halliru Usman, ya ce sun kafa dakarun ne da hadin gwiwar Ma’aikatar Gona domin ba da kariya ga dazuzzukan kiwo da gonaki da kuma kare sauran albarkatun noma.

Ya ce dakarun za su fara aiki ne da mutum 65 da suka samu horo a Jihar Katsina, kuma ana kan ba da horo ga sauran jami’ansu wadanda da zarar sun kammala za a tura su wuraren da suka dace

Ya ce za a horar da daruruwan dakarun tsaron rukuni-rukuni, don gudanar da wannan aiki; inda za a rarraba su a lungu da sakon jihar.

Malam Usman ya ce: “Wadannan dakaru sun samu horo ne ta fuskar kare dazuzzuka da tattara bayanan sirri da bada taimakon agajin gaggawa da kuma warware rikice-rikice, a Kwalejin Bayar da Horo kan Zaman Lafiya da Sasanta Rikice-Rikice da ke Jihar Katsina.”

Kwamandan ya ce manufar kafa dakarun ita ce domin  wanzar da zama lafiya kuma ta taimaka wa manoma da makiyaya don su zauna lafiya da juna yayin da suke gudanar da ayyukansu.

Ya ce dakarun za su kuma kasance masu shiga tsakani ko da za a samu rashin jituwa a tsakanin manoma da makiyaya yayin da kuma suke kare dazuzzuka da gonaki daga masu yin kutse bada izini ba a cikinsu.

Malam Usman ya yaba wa Gwamnatin Tarayya, saboda yadda ta bullo da wannan shiri mai nagarta da nufin kare rayuka da dukiyoyin jama’a musamman a wuraren da ake samun rikice-rikice a fadin kasar nan. Sannan ya yaba wa  Gwamnatin Jihar Bauchi saboda ci gaba da goyon bayan da take ba su a jihar.