Da Dumi Dumi

Hukumar DFID da MAFITA sun kashe Naira biliyan 16 wajen koya wa yara marasa galihu sana’o’i

Hukumar Bunkasa Kasashe ta Ingila (DFID) da Kungiyar MAFITA Mai aiki a Arewacin Najeriya sun kashe Naira biliyan goma sha shida don horar da yara marasa galihu da nakasassu da wadanda ba su kammala karatun sakandare ba saboda inganta rayuwarsu su zamo masu dogaro da kansu su kauce wa shiga miyagun ayyuka.

Hukumomin biyu sun ce sun gano a Arewa ana da yara sama da dubu 10, da ba su zuwa makaranta sakamakon haka ne wadancan kungiyoyin biyu suka fito da wannan tsari saboda sama wa yaran abin dogaro da kansu a kauce wa rashin gaskiya.

Shugaban Shirin Mai kula da jihohi hudu da suka Kano da Jigawa da Katsina da Kaduna, Malam Umar Nuhu Muhammed ya tabbatar da haka, inda ya ce a Jihar Jigawa an zabi kananan hukumomi uku da suka hada da Dutse da Hadeja da Kazaure inda ake ba wa yaran horo kan sana’ar walda da dinki da kafinta da kitso da kunshi da gyaran waya da gyaran inji da gyaran wutar lantarki da sauran sana’o’i.

Ya ce kungiyoyin sun dauki matakin haka ne da nufin hana yaran fadawa cikin wasu miyagun kungiyoyin da ka iya jefa su a cikin miyagun ayyuka da sace-sace tare da nufin inganta rayuwar yaran.

Shugaban ya kara da cewa yara dubu 20 aka bai wa horo a wadancan jihohin hudu cikin shekara hudu da kungiyoyin biyu suka yi suna ba da horon a nan Arewacin Najeriya.

ADVERTISEMENT

A jawabin Jami’in Shirin Mai kula da Jihar Jigawa, Malam Muhammad Bello, ya ce shirin koyar da sana’o’i na Master Craft yana kintsa yara masu karancin gata a jihar ya samu nasara saboda jihar da ta fara shirin kwanan nan ita ce ta zama zakara a kan jihohin Kano da Katsina da Kaduna wajen bai wa yaran horo.

Ya ce a Jihar Jigawa yara 1,712 suka samu horo a fannoni daban-daban daga kananan hukumomin da aka fara gwada shirin da su kuma lamari ne da ake tantance yaran sai an tabbatar su ba ’ya’yan kowa ba ne ake tallafa musu saboda su zama masu dogaro da kansu. Alhaji Bello ya ce Hukumar DFID da Kungiyar MAFITA ta Najeriya sun ware fam miliyan 38 ga wadannan jihohi hudu domin aiwatar da wannan shirin na tallafa wa marayu da marasa karfi a Arewacin Najeriya saboda a nan ne ake da matsalar koma bayan ci gaban rayuwa.

Share